Matan sojoji sun tallafa wa gidajen marayu a Borno

Tallafin ya hada da bada magungunan ga marasa lafiya kyauta a unguwar Shuwari, hanyar Baga, Maiduguri, da rabon kayan abinci ga gidajen marayu na  Fatima Orphanage da na Widows Educational Foundation Songhai, Maiduguri, da kuma Cibiyar bincike ta hadin gwiwa (JIC), da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri.

Matan sojoji sun tallafa wa gidajen marayu a Borno

Kungiyar Matan Hafsoshin Sojin Kasan Najeriya (NAOWA) ta ba da tallafin magunguna da kayan abinci ga gidajen marayu a Jihar Borno domin rage musu radadin rayuwa.

Tallafin ya hada da bada magungunan ga marasa lafiya kyauta a unguwar Shuwari, hanyar Baga, Maiduguri, da rabon kayan abinci ga gidajen marayu na  Fatima Orphanage da na Widows Educational Foundation Songhai, Maiduguri, da kuma Cibiyar bincike ta hadin gwiwa (JIC), da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri.

Shugabar kungiyar NAOWA reshen Runduna ta 7 da ke Barikin Maimalari a Maiduguri, Hajiya Aishat AGL Haruna, ta ce kungiyar ta bullo da wadannan tsare-tsare ne domin tallafa wa al’umma musamman wajen inganta lafiya, tsaftar muhalli.

Hajiya Aishat ta jaddada cewa manufofin kungiyar sun yi daidai da shirin rundunar sojin Najeriya na inganta walwalar sojoji da iyalansu da ma sauran al’ummar da ke kewaye da su.

“Wayar da kan jama’a zai  taimaka sosai wajen inganta lafiyar jama’a kuma zai zama taimako ga wannan matsalar tattalin arziki da ake ciki musamman wajen tunatar da su kan mahimmancin lafiya da kuma tsaftar muhalli.

“Bayar da tallafin abinci ga marayu da zawarawa shi ma yana da matukar muhimmanci kuma a matsayinmu na iyaye mata, muna  girmama tallafawa da kula da yaranmu,” in ji Aishat.

Shugabar ta yi alkawarin samar da karin tallafi ga gidajen marayun a bangarorin  ilimi da kiwon lafiya tare da karfafa gwiwar yaran da su tsaya tsayin daka don gina makomarsu.

Uwargidan gidauniyar marayu ta Fatima, Fatima Babagana da shugabar gidauniyar Dennis Yusuf Wuga sun yaba da wannan karimcin inda suka yi addu’ar Allah Ya saka wa Kungiyar ta  matan sojojin.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa