Najeriya A Yau: Kama Mana Maza Ya Sa Mu A Tsaka Mai Wuya —Matan ’Yan Canji
Suna neman Sarkin Kano ya sanya baki a bayyana musu halin da mazajen nasu suke ciki
Domin sauke shirin latsa nan
A ranar Alhamis ce matan ’yan canji daga Kasuwar Wapa da aka tsare suka ziyarci Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin neman ya sanya baki a bayyana musu halin da mazajen nasu suke ciki.
Shirin Najeriya A Yau ya dauko cikakken rahoton halin da iyalan su wadannan ’yan canji suke ciki shekara guda tun bayan tsare su.