Matan yanzu sun fi son kudi fiye da komai a soyayya —Bincike

A binciken da aka gudanar a dandalin sada zumunta mutane sun bayyana ra’ayoyinsu a kan dalilan da za su sa mace ta so namiji.

Matan yanzu sun fi son kudi fiye da komai a soyayya —Bincike

Ma’aurata

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da Aminiya ta gudanar ya gano cewa da yawa daga cikin ’yan mata a wannan zamani sun fi son kudi fiye da komai daga bangaren maza a zamantakewar soyayya.

Binciken dai ya  gudana ne a dandalin  sada zumunta na Facebook, inda mutane suka bayyana ra’ayoyinsu a kan dalilan da za su sa mace ta so namiji.

Binciken ya bi diddigi ra’ayoyin jama’a kan dalilan da ke iya sa mace ta so namiji, inda yawancin mutanen da suka yi tsokaci a kai sun bayyana cewa tabbas yanzu  mata a wannan zamani idan ka ga sun so namiji to yana da abin hannunsa.

Abubakar Yahaya… cewa ya yi, “’Kudi’ kai-tsaye ba tare da kara wani abu ba,” inda nan take Kabeer Abdulmumeen ya ce, “Ina tare da kai wannan shi ne amsar [wannan] tambayar kawai. Kashi 10 cikin 100 ne kawai za su so ka ba don abin hannunka ba.

Ya kara da cewa “Dukiya mana. Ko akwai wani abu a zamanin nan da yake burge mata a gun namiji sama da wannan?”

Abba Best, kuma cewa ya yi, “Matan da nasaba, addini, tarbiyya, sana’a ke sa su so namiji, amma matan yanzu sai kudi, da Dala su ne dalili.

“Bayan kasancewa mutum yana da kudi, har ila yau, ya kasance bai damu da abin hannun nasa ba, ma’ana zai iya bayarwa a kowane lokaci aka bukata.”

Sai dai wasu na ganin ba wai iya kudi ne dalilin da ya ke sa mata su so namiji ba, wasu abubuwa kamar tsafta, nutsuwa, hankali kan sa mace ta so namiji kamar yadda Muhammad Muhammad ya bayyana.