Matana ba su san ina fashi ba sai bayan an kama ni – Omoboye

’Yan fashin da rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame kan zargin yi wa bankuna biyu fashi a yankin Ikorodu da ke jihar kwanan nan sun ci gaba da bayyana yadda suka shirya fashin, inda daya daga cikinsu mai suna Monday Omoboye ya ce matansa biyu ba su taba sanin yana fashi da makami ba […]

Matana ba su san ina fashi ba sai bayan an kama ni – Omoboye
Matana ba su san ina fashi ba sai bayan an kama ni – Omoboye

’Yan fashin da rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame kan zargin yi wa bankuna biyu fashi a yankin Ikorodu da ke jihar kwanan nan sun ci gaba da bayyana yadda suka shirya fashin, inda daya daga cikinsu mai suna Monday Omoboye ya ce matansa biyu ba su taba sanin yana fashi da makami ba sai bayan da aka kama shi.

Omoboye wanda ya yi furucin yayin da manama labarai suke yi masa tambayoyi a harabar rundunar ’yan sandan Jihar Legas, ya bayyana cewa ya dade yana fakewa da sana’arsa ta tukin jirgin ruwa yana fashi.
“Asalin sana’ata ita ce tukin jirgin ruwa, da ita mutane suka san ni ko da matana ba su san na shiga harkar fashi ba don ina fakewa ne da sana’ata don kada mutane su gane. Na dade ina shiga fashi da makami daban-daban a wurare da dama na Jihar Legas.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Ni na dauke su a jirgi zuwa wurin da muka yi fashi a Lekki da wanda aka yi a unguwar Ijede da unguwar Ipakodo, inda muka fasa bankuna kwanan nan. Na samu Naira dubu 400 a fashin da muka yi a yankin Lekki sannan na samu miliyan biyu a wanda muka yi a Ijade sai kuma na yankin Ipakodo, shi ma na samu Naira miliyan biyu inda na sayi mota ta Naira miliyan daya da dubu goma sha biyar’.
Ya bayyana cewa a fashin da suka yi kwan nan, da ’yan sanda sun biyo da sun kama su. “Lokacin da muka yi fashin muka shiga jirgin ruwa sai jirgina ya lalace. Da jami’an tsaro sun biyo mu da sun kama mu don nan muka tsaya har sai da shugabanmu ya kira wani matukin jirgin ya zo ya dauke mu. Dukkanmu mun tsure mun dauka za a kama mu.” Inji shi.
’Yan fashin da aka kama sun hada da Omoboye wanda ake yi wa lakabi Alarm Blow dan shekaru 39 sai Bright mai shekaru 25 sai Ikuesan mai shekaru 37 da kuma Abiwa mai shekaru 20 da haihuwa.
daya daga cikin ’yan fashin mai suna Bright ya bayyana cewa mutum 18 ne suka yi fashin bankunan da ke yankin Ikorodu a karkashin jagorancin shugabansu mai suna Miliyan.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Mista Kayode Aderanti, ya bayyana cewa asirin ’yan fashin ya tonu ne a lokacin da sojoji da ke bincike suka kama daya daga cikinsu da sababbin kudi.
Ya ce bayan da aka tsananta bincike a kan mutumin sai aka gano cewa irin kudin da aka sata ne a bankunan da aka yi wa fashi a Legas.
“Nan take suka sanar da mu inda muka tura jami’anmu suka kama mutumin daga bisani muka kama sauran a maboyarsu daban-daban.” In ji shi.