Matar aure ga kotu: Ba zan sake cizon mijina ba

Wata matar aure mai suna bictoria Yisa, ’yar shekaru 33 da haihuwa ta yi alkawari a gaban kotun gargajiya ta Ojo da ke Legas cewa, ba za ta sake cizon mijinta Samuel Yisa a duk lokacin da suke kaure da fada a tsakaninsu ba. Matar wacce ta fashe da kuka a lokacin da take kare […]

Matar aure ga kotu: Ba zan sake cizon mijina ba
Matar aure ga kotu: Ba zan sake cizon mijina ba

Wata matar aure mai suna bictoria Yisa, ’yar shekaru 33 da haihuwa ta yi alkawari a gaban kotun gargajiya ta Ojo da ke Legas cewa, ba za ta sake cizon mijinta Samuel Yisa a duk lokacin da suke kaure da fada a tsakaninsu ba. Matar wacce ta fashe da kuka a lokacin da take kare kanta dangane da karar da mijinta ya shigar, yana neman kotun ta raba auren nasu a dalilin yawan cizon jikinsa da take yi. Ta shaida wa alkali cewa daga yanzu za ta zama mutunniyar kirki da hakuri ba tare da fuskantar mijinta da fada ba. “Don Allah yallabai kada ka kashe wannan aure, ka taimaka wajen ceto auren daga mutuwa. Ina tabbatar maka cewa daga yanzu na canza salon zamantakewa da mijina. Ba zan sake kasancewa mafadaciya ba kuma ba zan sake maimaita irin wannan mummunan hali a tsakanina da mijina a nan gaba ba. Ina kaunar mijina, don Allah a ba shi hakuri ya yafe mani.” Inji ta.

Tun farko Mista Samuel Yisa mai shekaru 44 ya roki kotun ta kashe wannan aure da suka shafe shekaru 10 a tsakaninsa da matarsa a dalilin yawan cizonsa da take yi a duk lokacin da aka samu sabanin zamantakewa a tsakaninsu. Ya shaida wa kotun cewa: “Wannan mata mafadaciya ce, domin a duk lokacin da muka samu rashin jituwa da ita sai ka ga ta fara matsowa kusa da ni domin cizon wani sashe na jikina. Akwai lokacin da aka kwantar da ni a asibiti da aka yi mani maganin mummunan raunin a hannuna, a dalilin gartsa mani cizo. An sha yin zama a tsakanin iyayenta da nawa domin yi mata nasiha a game da wannan al’amari amma har yanzu ta ki dainawa. Saboda haka a yanzu ni dai na gaji da irin wannan hali nata kuma nake rokon kotu ta raba auren.”
Bayan sauraron bayanan miji da mata, mukaddashin alkalin kotun, Mista S. B. Giwa, ya nemi su koma gida su sasanta tsakaninsu har zuwa ranar 23 ga watan gobe, inda za su shaida wa kotun sakamakon irin zaman da suka yi.