Matar aure ta banka wa budurwar mijinta wuta

Ta watsa wa budurwar mijinta fetur sannan ta cinna mata wuta a yayin wata takaddama

Matar aure ta banka wa budurwar mijinta wuta

‘Yan Sanda a yayin bincike

’Yan sanda sun cafke wata matar aure mai shekara 32 bayan ta banka wa daduron mijinta wuta.

Matar mai ’ya’ya uku ta watsa wa farkar mijin nata fetur ne ta cinna mata wuta, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarta.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da cafke matar auren ga manema labarai a garin Abeokuta a ranar Juma’a.

A cewar Oyeyemi, an cafke matar ne bayan mijin wadda aka kashe din ya shigar da kara a ofishin ’yan sanda da ke Ota a jihar.

Mijin wadda aka kashe din ya shaida wa ’yan sanda cewa matar tasa ta bar gidanshi zuwa gidan daduron nata ne jim kadan bayan ya fara zargin tana bin maza.

“Da na tunkare ta da maganar, abin mamaki, sai kawai ta kwashe kayanta daga gidana ta koma gidansa da zama,” inji mijin nata.

Ya ce ana cikin haka ne ranar 14 ga Nuwamba 2021 rikici ya kaure tsakanin matar tasa da matar daduron nata, inda matar daduron ta watsa mata fetur ta kuma cinna mata wuta.

“’Yan uwanta sun garzaya da ita zuwa asibiti, a can ne kuma ta ce ga garinku nan,” a cewarsa.

Kakakin ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin ne suka garzaya suka cafko matar auren da ake zargin tana kokarin tserewa.

“An mika ta ga sashen binciken manyan laifuka don gudanar da bincike yadda ya kamata.

“Da aka titsiye matar ta amsa aikata laifin amma ta ce ba a cikin hayyacinta take ba a lokacin da hakan ta faru,” a cewar Oyeyemi.