Matar aure ta banka wa mijinta wuta
Matar ta watsa wa mijin nata fetur ta cinna masa wuta ne saboda ya shiga dakin kishiyarta, sun tattauna da ita.

An gurfanar da wata matar aure a kotu kan zargin ta da cinna wa mijinta wuta a Jihar Kano.
Ana zargin matar ta watsa wa mijin nata fetur sannan ta cinna masa wuta ne saboda ya shiga dakin sabuwar amaryarsa, suna tattaunawa da ita.
Shaidu sun bayyana cewa wadda ake zargin ta yi aika-aikan ne bayan ta nemi mijin nata ya fito daga dakin amaryar tasa amma ya ƙi amincewa.
Magidancin ya samu munanan kuna a sakamakon wutar da matar tasa ta yi masa.
Lauyar Gwamantin Jihar Kano, Saima Garba, ta karanta wa matar takardar tuhumar aikata kisa da ake mata, amma ta musa.
Daga nan alƙalin kotun Majistare mai Lamba 25, Halima Wali, ta ba da umarnin tsare matar a gidan yari sannan ta ɗage sauraron shari’ar da makonni biyu.