Matar aure ta cafke mazukatar mai fyade har ya mutu

Wata matar aure mai kimanin shekara 40 mai suna Ladi dandare da ke kauyen Gidan Kaso a karamar Hukumar Birnin Magaji a Jihar Zamfara ta cafke mazakutar wani mai shekara 45 da ya yi yunkurin yi mata fyade har ya mutu.Marigayin ya yi yunkurin yi mata fyade ne a gidan mijinta da daddare bayan ya […]

Matar aure ta cafke mazukatar mai fyade har ya mutu
Matar aure ta cafke mazukatar mai fyade har ya mutu

Wata matar aure mai kimanin shekara 40 mai suna Ladi dandare da ke kauyen Gidan Kaso a karamar Hukumar Birnin Magaji a Jihar Zamfara ta cafke mazakutar wani mai shekara 45 da ya yi yunkurin yi mata fyade har ya mutu.
Marigayin ya yi yunkurin yi mata fyade ne a gidan mijinta da daddare bayan ya yi mata barazanar kisa da wuka.
Wani dan uwan matar mai suna Kabir Sani ya ce, marigayin mai suna Ibrahim wanda ake yi masa lakabin dan Duniya dan banga ne a kauyen dandare, kuma ya sha yunkurin yi mata fyade, har ta kai kararsa wurin dagacin kauyen, inda aka kira shi aka gargade shi kan ya daina ko ya fuskanci hukunci mai tsanani, a lokacin dai ya musanta batun yunkurin yin fyaden a fadar dagacin.
dan Duniya yana da mata uku da ’ya’ya masu yawa, inda a ranar da zai gamu da ajalinsa, sai ya fita daga gidansa dauke da wuka, sannan ya shiga gidan matar, inda ya yi mata barazanar kisa idan ba ta amince masa ba.   
Kabir ya ce, “Sai ta amince, sannan ta ce ya tube kayansa, bayan ya tube ne, sai ya kwantar da ita, sai dai abin da bai sani ba ashe tana fakonsa ne, bai ankara ba sai ta cafke mazakutarsa tun yana ihu har a karshe ya mutu. An ji lokacin da yake ihu don makwabta su kawo masa agaji amma babu wanda ya zo.”
Ya kara da cewa, “Bayan ta tabbatar ya mutu ne sai ta ruga gidan dagacin kauyen, ta sanar da shi abin da ya faru. Daga nan ya umarci sauran ’yan bangar su bi ta don gane gaskiyar abin da ya faru. Bayan sun tabbata ya mutu sai aka kai gawarsa asibiti don a yi bincike, daga baya aka binne shi.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara, DSP Lawal Abdullahi ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce har yanzu ’yan sanda na gudanar da bincike a kai.
Ya ce: “Matar tana wurin ’yan sanda, duk da cewar ta yi hakan ne don kare kanta, amma duk da haka muna ci gaba da bincike. Idan mun kammala za mu mika al’amarin zuwa Ma’aikatar Shari’a ta Jiha don ganin yadda za a bullo wa al’amarin.”