Matar aure ta kashe agolarta a Adamawa
Jami’an tsaro sun cafke wata matar aure da ta lakada wa agolarta dukan tsiya har ta mutu a Jihar Adamawa. Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, DSP Sulaiman Nguore, ya ce matar da aka kama a yankin Mayobelwa ta hana yariyar da ta rasu abinci. An cafke matar da ta kashe ’ya’yanta 2 a Kano […]
Jami’an tsaro sun cafke wata matar aure da ta lakada wa agolarta dukan tsiya har ta mutu a Jihar Adamawa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, DSP Sulaiman Nguore, ya ce matar da aka kama a yankin Mayobelwa ta hana yariyar da ta rasu abinci.
Ya shaida wa Aminiya a birnin Yola cewa ’yan sanda sun kama matar ne ranar Alhamis bayan makwabta sun kai rahoton kashe agolarta tata.
DSP Nguore ya ce ana Sashen Binciken Miyagun Laifuka na rundunar na kammala bincike za a gurfanar da matar a gaban kuliya.
A yayin da Aminiya ta nemi jin ta bakin matar, ta musanta zargin da ake mata na kashe yarinyar.
Ta ce yarinyar ta dade tana fama da zazzabin kuma mahaifinta ya ki bayar da kudin sayen magani.
“Ni ban kashe ta ba, abin da ya faru shi ne Walida tana son shiga gidan makwabta saboda haka sai na aiki daya daga cikin ’ya’yana su kira ta.
“Bayan zuwanta sai na dungure mata goshi da yatsata domin na nuna mata kuskurenta, sai kawai ta fadi kasa.
“Sanin cewa ba ta jin dadi ya sanya na yi gaggawar zuwa gidan wani dan uwana sai aka yi rashin sa’a na tarar baya nan.
“Bayan na dawo gida sai na riski daya daga cikin makwabtana kuma aka ce ai yarinyar ta rasu.
“Mijina wanda shi ne ummulhaba’isin wannan lamari an kama mu tare da shi, kuma bayan kwana daya aka sake shi”, inji ta.