Matar aure ta kashe danta, ta kona mijinta

Ta kashe jaririn da ta haifa ta kuma binne shi a sirrance, wata takwas da suka wuce, saboda tsabar damuwa.

Matar aure ta kashe danta, ta kona mijinta

Jami’an ‘Yan sanda

Wata matar aure ta kashe dan da ta haifa sannan ta antaya wa mijinta tafasasshen ruwa.

Matar mai shekara 43 ta yi aika-aikan ne bayan da ta zargi mijin nata da tsananin shan giya da kuma watsi da kula da iyali.

Magidancin ya shiga caji ofis ne a guje, jikinsa duk kuna, ya yi karar cewa matarsa ce ta yi mana haka bayan fada ya kaure tsakaninsu, bisa zargin cewa shi dan giya ne.

Suna cikin sa-in-sar ne ta dauko tukunya cike da tafasasshen ruwa a kwara masa.

Bayan damke matar, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta ce wadda ake zargin ta kashe jaririn da ta haifa ta kuma binne shi a sirrance, wata takwas da suka wuce, saboda tsabar damuwa.

Kakakin Rundar, Abimbola Oyeyemi, ya ce, “Da aka tsare matar ta bayyana yadda mijinta ke dawowa gida a buge kuma ba ya ba da komai na kula da ita ko yara.

“Ta ci gaba da cewa a ranar da abun ya faru, mijin ya dawo gida ne a buge kamar yadda ya saba, amma da ta fara korafi kan buguwarsa, sai ya fara zagin ta da iyayenta wanda hakan ya fusata ta.”

Oyeyemi ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Edward Awolowo Ajogun,  ya ba da umarni Sashen Binciken Manyan Laifuka su ci gaba da bincike matar sannan a gurfanar da ita a gaban kotu.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya