Matar aure ta kashe mijinta da tabarya

Mutuwar magidancin ta haifar da takaddama tsakanin jama’ar gari da ’yan sanda

Matar aure ta kashe mijinta da tabarya

Jama’ar gari na zargin wata matar aure da aika mijinta barzahu ta hanyar buga masa tabarya a kokon kansa a garin Akungba-Akoko da ke Jihar Ondo.

Mutuwar magidanci cikin dare ta haifar da takaddama a tsakanin al’ummar garin da ’yan sandan jihar.

Aminiya ta gano cewa, wasu makwabtan marigayin sun zargi matarsa da kashe shi ta hanyar buga masa tabarya a kokon kansa a lokacin da gardama ta murtuke a tsakaninsu cikin daren ranar Lahadi.

Wata majiya a makwabtan ta ce matar ta dade tana zargin mijinta da neman mata, lamarin da ya kai ta daukar matakin hallaka shi ta hanyar buga kwada masa tabaryar a kokon kansa a lokacin da yake bacci a cikin gidan da suke zaune.

Majiyar ta ce daya daga cikin dattawan gari, Cif Awesu, ya tabbatar da cewa matar ta dade tana zargin mijinta da neman matan banza.

An gayyaci sarkin al’ummar Musulmin garin Akungba a Karamar Hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma zuwa gidan marigayin, inda ya taras da magidancin kwance cikin jini a cikin gidansa, aka garzaya da shi zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Majiyar ta ce makwabta da al’ummar garin sun yi tir da daukar matakin kashe mijinta da wannan mata ta yi.

Sun ce magidancin mutumin kirki ne musamman a kan kyautata wa iyalinsa da suke cewa ya saya wa wannan mata sabuwar mota kuma ya gina mata sabon gida bayan daukar dawainiyar ta da ’yan uwanta da, ta yanke shawarar raba shi da rayuwarsa kan zargin da bai tabbata ba.

Aminiya ta gano cewa mutuwar mutumin ta haifar da takaddama a tsakanin al’ummar garin da ’yan sanda.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar Seidu Jamiu, amma ta ce ba ta kama kowa ba tukuna musamman saboda kasancewar matar da kanta ta kai rahoto ofishin ’yan sanda cewa wasu mutane sun kashe mijinta cikin daren rana Asabar.

Kakakin ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta ce “ba za mu iya tabbatar da cewa matar marigayin ce ta kashe shi ba saboda ita ce da kanta ta kai rahoton mutuwarsa a ofishin ’yan sanda da safiyar ranar Asabar.

“Ta shaida wa ’yan sanda cewa wasu mutane ne suka yi wa mijinta kisan gilla a cikin daren.”

Jami’ar ta kara da cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano gaskiya da kuma kama masu hannu a ciki.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania