Matar aure ta kashe mijinta da wuƙa a Yobe

Matar ta ce ba ta yi niyyar kashe mijinta ba sai dai ta daɓa masa wuƙa ne a dalilin dukan tsiya da yake mata.

Matar aure ta kashe mijinta da wuƙa a Yobe

Ana zargin wata matar aure, Zainab Isa, mai kimanin shekara 22 ta kashe mijinta Ibrahim Yahaya Mai kimanin shekara 25 mazaunin unguwar Abbati cikin garin Damaturu a Jihar Yobe.

Lamarin ya faru ne sakamakon taƙaddamar da ta auku tsakanin ma’uaratan ranar Talata wadda ya kai ga ta soka wa mijinta nata wuƙa kuma nan take ya ce ga garinku nan.

Wata majiyar da ke unguwar ta Abbari ta bayyana cewar, ma’auratan sun daɗe suna takun saƙa a tsakaninsu, amma abinka da ajali taƙaddamar ƙarshen ita ce ta kai ga matar ta aika da mijin nata lahira.

Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta bakin kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim ta tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari.

Wakilinmu ya ruwaito cewa DSP Dungus ya yi manema labarai ƙarin haske kan faruwar lamarin da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar 26 ga Yunin bana a hedikwatar ’yan sanda ta C Division a da ke birnin Damaturu.

Kakakin ’yan sandan ya ce sun samu ƙorafin faruwar lamarin daga wani maƙwabcin ma’auratan da ke unguwar ta Abbari.

Ya ce makwabcin ya bayyana musu cewar ma’auratan sun yi musayar yawu a tsakaninsu lamarin da ya rikiɗe zuwa rikici.

Bayanai sun ce ana tsakar jayayyar ce sai matar ta yi amfani da wuƙa ta daɓa wa mijin a ƙirji, kuma daga baya ya mutu sakamakon mummunan rauni da ya samu kafin tawagar ‘yan sanda ta ƙaraso gidan.

DSP Dungus tuni aka miƙa matar sashen binciken manyan laifuffuka domin ɗaukar matakan da suka dace gabanin gurfanar da uta a gaban kuliya.

A bayanin da ta yi wa ’yan sandan, matar ta ce ba ta yi niyyar kashe mijinta ba, sai dai ta daɓa masa wuƙa ne domin ta kare kanta sakamakon dukan tsiya yake mata a lokacin faruwar lamarin duk da cewa ba ta gama samun sauƙi daga tiyatar da aka yi mata kwanan nan a dalilin haihuwar da ta yi ƙasa da wata guda.

Ta ci gaba da cewa “mun sha fuskantar matsaloli da tashin hankali a rayuwar aurenmu.

“Kusan kullum sai mun yi rikici da shi [mijin nawa] musamman idan na nemi kuɗin cefanen abinci tun lokacin aurenmu har bayan haihuwar ɗanmu na farko da na biyu.”

Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Garba Ahmed, ya buƙaci ma’aurata da su riƙa miƙa rahoton  duk wani nau’i na cin zarafinsu da suke fuskanta a tsakaninsu ga mahukunta mafi kusa.

Kwamishinan ya ce wannan ita kaɗai ce hanyar da za a samu mafita mai ɗorewa ko kuma a kai ƙara kotu ko kuma miƙa wa ’yan uwa mafi kusa ƙorafi domin a yi musu sulhu maimakon ɗaukar mummunan mataki irin haka.

Ya kuma yi kira da umartan ’yan uwa da su riƙa  magance matsalolin da suka shafi zamantakewar aure kan lokaci don hana ta’azzara daga ƙananan rikice-rikice zuwa manya kamar kisan kai.

Ƙoƙarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin ‘yan uwan ɓangarorin biyu ya ci tura.

Dangin waɗanda abin ya shafa sun ƙi cewa uffan musamman ganin cewar ma’auratan ’yan uwan juna kasancewar mahaifansu na da dangantaka ta kut-da-kut.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka