Matar aure ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa

Wata matar aure ta yi wa kishiyarta wanka da tafasashshen ruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar kishiyar ta samu munanan raunuka a Kano. Matar, ‘yar kimaninn shekaru 26 mai suna Zulaihat Nasir, ta watsa wa kishiyarta mai suna Nafisa Isa ruwan ne saboda wani fada da suka yi. Dukansu mata ne ga Ibrahim Sabo, mazaunin […]

Matar aure ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa

Wata matar aure ta yi wa kishiyarta wanka da tafasashshen ruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar kishiyar ta samu munanan raunuka a Kano.

Matar, ‘yar kimaninn shekaru 26 mai suna Zulaihat Nasir, ta watsa wa kishiyarta mai suna Nafisa Isa ruwan ne saboda wani fada da suka yi.

Dukansu mata ne ga Ibrahim Sabo, mazaunin unguwar Zango da ke cikin birnin Kano.

Yanzu haka Nafisa na can tana jinya a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da ke Kano, sakamakon mummunar konewar da ta yi a kanta da kuma kirjinta.

Ita kuma Zulaiha da ake zargi na can a komar ‘yan sanda inda ta ce ta watsa wa Nafisa tafasashshen ruwan ne saboda ta kulle ta a daki tare da barazanar banka wa dakin wuta.

Ta ce Nafisa ta kulle ta a daki tun kimanin 4:00 na yamma kuma ba ta sami damar fitowa ba sai da mijinsu ya dawo gida cikin dare.

Ta kara da cewa a kan haka ne ta yanke shawarar sheka wa kishiyar ruwan don ta huce takaici a matsayin ramuwa.

“Mun yi fada da ita ne, to bayan na shiga daki kawai sai ta sa makulli ta rufe ni a ciki tana barazanar za ta banka wa dakin wuta.

“Tun kimanin karfe hudu na ke kulle a dakin kuma ba a bude ni ba sai da Magariba lokacin da mai gidanmu ya dawo. Hakan ne ya sa na hassala na kuma sha alwashin daukar fansa ta hanyar watsa mata ruwan,” inji ta.

To sai dai ko da jami’an ‘yan sanda suka cika hannu da ita, Zulaiha ta yi da-na-sanin abin da ta aikata.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce lamarin ya faru ne da misalin 11 na safiyar ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu.

Ya ce tuni Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Habu Sani ya yi umarnin a mika batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar domin fadada bincike.

Ya kara da cewa da zarar an kammala binciken za su tura duk wanda ake zargi da laifi gaban kuliya don ya girbi abin da ya shuka.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara