Matar aure ta lakada wa mijinta duka

Matar ta buga wa mijinta fasasshe kwana a kai sannan ta farfasa motocinsa

Matar aure ta lakada wa mijinta duka

Kotu

An gurfanar da wata matar aure a gaban kotu saboda ta lakada wa mijinta duka a Jihar Legas.

Jami’an tsaro sun gurfanar da matar mai shekaru 34 a gaban alkali ne bayan ta yi  amfani da wani fasasshen kwano wajen dukan mijin nata.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Courage Ekhueorohan, ya shaida wa kotun majistare da ke yankin Surulere cewa matar ta kwada wa mijin nata fasasshen kwanon ne a kansa.

Matar ta yi wa mijin nata wannan aika-aika ne bayan an kai mata tsegumi cewa yana kawo matan banza gidansu na aure.

Mai gabatar da kara ya ce, matar ba ta tsaya nan ba, sai da ta farfasa gilasan motocin mijin nata guda biyu.

A cewarsa, a halin da ake ciki ma’auratan sun daina zama tare kuma sun fara shirye-shiryen kashe aurensu.

Bayan sauraron karar ne alkalin kotun, Mai Shari’a O.O. Otitoju, ta ba da belin wadda ake kara a kan kudi N200,000, da sharadin za ta kawo ’yan uwanta na jini guda biyu da za su tsaya mata.

Daga nan aka dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Mayu mai kamawa. (NAN)