Matar aure ta tsara sace kanta a Neja
Ana zargin wata matar aure mai suna Habiba Usman mai shekara 20 da tsara sace kanta da niyyar amsar kudin fansa daga mijinta, Malam Usman Alfa. Habiba wadda aka ce tana da juna biyu, ta bar gidan mijinta da ke unguwar Beji a Karamar Hukumar Boos da ke jihar da niyyar zuwa awon ciki a […]
Gwwamna Jihar Neja Abubakar Sani Bello
Ana zargin wata matar aure mai suna Habiba Usman mai shekara 20 da tsara sace kanta da niyyar amsar kudin fansa daga mijinta, Malam Usman Alfa.
Habiba wadda aka ce tana da juna biyu, ta bar gidan mijinta da ke unguwar Beji a Karamar Hukumar Boos da ke jihar da niyyar zuwa awon ciki a Babban Asibitin Minna ne a ranar 28 ga Disamban da ya wuce amma ba ta dawo ba.
Wata majiya ta ce bayan kokarin gano inda take ya ci tura, sai mijin ya sanar da iyayen matar da dangi wadanda suka tashi gadan-gadan wajen binciko duk inda suke tunanin za ta je ba tare da nasara ba.
“Can dare sai wani ya kira mijinta a waya yana neman kudin fansa Naira miliyan hudu kafin a sako ta,” inji majiyar.
An ce mijin da hadin gwiwa da iyalansa sun yi ta roko har aka rage kudin fansar zuwa Naira dubu 150, sannan suka biya aka sako matar.
Sai dai mijin ya riga ya sanar da ’yan sanda a Beji kan bacewar matarsa, kuma Aminiya ta samu labarin cewa ’yan sanda sun bi diddigin layin da aka kira har zuwa Karamar Hukumar Sarkin Pawa, amma sai aka ce wanda ake zargin ya koma yankin Tunga da ke Minna bayan karbar kudin fansar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, DSP Mohammed Dan-Inna Abubakar ya ce ’yan sanda sun fara bincike jim kadan da samun korafin. “Nan take masu bincike daga bangaren yaki da satar mutane da jami’an leken asiri (SIB) da ofishin ’yan sanda na Bosso suka fara aikin binciken sirri, inda suka gano wadanda ake zargin a Sarkin Pawa da Tunga inda aka kama mutum biyu da syuka hada da Umar Abubakar mai shekara 28, wanda ya fito daga Karamar Chanchaga da ke jihar da Musa Abubakar mai shekara 22 na Unguwar Sauka-Ka-Huta da ke Minna ibisa zargi da hannu a lamarin. Kuma a yayin bincike ne aka gano wadda aka ce an sacen ta hada baki ne da mutum biyun da niyyar ta samu kudi daga mijinta,” inji DSP Abubakar.
Ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun amshi Naira dubu 150 kafin su sako matar. Kuma ya ce an samu Naira dubu 140 da 850 daga wadanda ake zargin su uku don zama shaida. Ya ce suna ci gaba da bincike kan lamarin.