Matar Bahaushe ko matar zamani?

Maganar farko wadda ita ta fi yawa a wancan rubutu, kuma a kanta marubucin ya fi maida hankali domin ita ta janyo duk sauran tsokacin da aka yi har zuwa karshen rubutun, ita ce maganar da wata mata ta yi game da karancin rigunan da matar Bahaushe ke sanyawa a rayuwa. Kuma a irin ra’ayin […]

Matar Bahaushe ko matar zamani?
Matar Bahaushe ko matar zamani?

Maganar farko wadda ita ta fi yawa a wancan rubutu, kuma a kanta marubucin ya fi maida hankali domin ita ta janyo duk sauran tsokacin da aka yi har zuwa karshen rubutun, ita ce maganar da wata mata ta yi game da karancin rigunan da matar Bahaushe ke sanyawa a rayuwa. Kuma a irin ra’ayin matar da ta turo da tambihin ta gamsu cewa wadannan su ne dalilan da ke jefa matar Bahaushe cikin matsalolin rayuwa. Kamar yadda ta tambaya, me ya sa matan Hausawa rigunan da suke sanyawa ba su da yawa ko kuma suke sanya rigunan ba daidai ba?
Amsar da zan ba wannan matata a nan ita ce, tara yawan rigunan a wajen matar Bahaushe ba shi ne ya fi muhimmanci ba. Mafi muhimmanci shi ne ta sanya rigar mutunci a matsayin shimi ko singileti, koyaushe tana manne da jikinta. Hakan ba zai hana ta sanya duk wata riga ba a rayuwa. Idan aka ce matar Bahaushe ba za ta sanya rigar aure da ta haihuwa ba har sai ta sanya riguna biyar kamar yadda marubuciyar ta jero, ana nufin a daina auren mace a lokacin da take tsakiyar kuruciya sai ta fara gajiya ke nan. Domin idan muka duba yawan shekarun da mace take yi kafin ta iso wannan matakin za mu fitar da sakamako kamar haka:
Rigar firamare: shekara 5 zuwa 11/12
Rigar sakandire: shekara 12 zuwa 16/17
Rigar jami’a: shekara 17 zuwa 22/23
Rigar hidimar kasa: shekara 23 zuwa 24
Wannan siyakin da na kawo shi ne ga wadda ba ta taba samun matsalar maimaita aji ko jinkirin tafiya makaranta saboda rashin kudi ko rashin daukarta da wuri ba. Sannan ba ta samu matsalar gyaran jarrabawa ba ko yajin aiki. Haka kuma shekara hudun jami’a ga wadda take karanta fanni mai shekara hudu ke nan a makarantar da ake iya kammala ta a hakan in har komai ya tafi mata daidai.
Abin da yake faruwa a nan shi ne, duk matar da ba ta nemi rigar aure ba sai bayan da ta kai wannan matakin, to kuma ba za ta samu rigar a arha ba. Dole sai ta tara kudin sayen rigar wanda hakan zai sanya sai ta nemi aiki ta fara daukar albashi, sannan ta yi asusun sayen rigar aure. Wannan zai sake daukarta wasu shekaru ke nan. Kada fa a manta kullum tsufa take kara yi ba komawa cikin kuruciya ba.
Idan kuma aka dauki yarinyar da ta cire rigar sakandire, galibi a daidai wannan gabar maza suna wawarta, don haka za a yi ta kawo mata rigunan aure iri-iri, sai wanda ta zaba. A daidai wannan gabar ita da iyayenta suna da damar zabin wanda ya zo da rigar da ta fi aminci, kuma ta fi dacewa da ita. Idan ta yi sakaci wannan lokacin ya wuce ba ta zabi mai kyau ba, to fa lokacin da ta zo tana neman rigar ido a rufe, duk wadda ta samu ko ba ta dace da ajinta ba, dole ita za ta saya komai rashin kyawunta. Don kuwa ba a zaben ruwan kashe gobara.
Kafin in je ga amsa maganar wannan baiwar Allah ta gaba, ni kuma ina bukatar karin haske game da ‘sauran matan duniya’ da take nufi cikin maganarta da take so matan Hausawa su yi koyi da su? Kuma me suka fi matar Bahaushe da shi ta bangaren mutunci ko jin dadin rayuwa?  
Kafin in samu wadannan amsoshin bari in je ga maganarta ta gaba yadda ta kawo matsalar  “haihuwar yuyuyu” da matar Bahaushe take yi, musamman matan karkara.
Mu dai a kasar nan, idan aka kwatanta wahalar da yawancin matan sauran kabilu suke sha tun daga na birni har na karkara, za a samu matar Bahaushe ta fi samun saukin rayuwa, musamman wadda ta sanya rigar aure da wuri. Domin kuwa matan kabilu da yawa a kasar nan su, su ke daukar nauyin duk wata dawainiyar kansu da ta mijinsu da ’ya’yansu. Mace za ta je gona ta yi aiki a biya ta ko ta noma gonar mijinta domin su samu abin da za su ci ko su sayar. Ita za ta je rijiya ko rafi ta debo ruwa domin amfanin gida. Ita za ta je shago ta wuni domin samun abin da za su rufa asirin iyali. Kada a manta bayan ta nemo ita take da alhakin girkawa domin kowa ya ci a gidan. Sannan fa ita ce mai daukar ciki da haihuwa tare da raino har zuwa daukar nauyin abin da ta haifa. ’Yan gata a cikin irin wadannan matan su ne wadanda ake raba dawainiyar gida tsakanin mijin da matar. Idan ya kawo wani abu cikin abin da yake samu ita ma ta kawo nata.
Idan aka koma bangaren matar Bahaushe, na san za a gamsu cewa yawancin wadancan wahalhalun da na lissafa matar Bahaushe ba ta san su ba. Abin da ta sani shi ne maigida ya fita ya nemo ita kuma ta girka. Hidimar daukar ciki da haihuwa kuma dama wannan nata ne a duk yadda ta samu kanta. Abin da ya saura mata shi ne, yanayin kulawa da kanta da yaranta ta bangaren lafiya da tarbiyyarsu. A bangaren lafiya, ya kamata mu tuna cewa, ita mace a lokacin da take da kuruciya ta fi jure wa daukar ciki da haihuwa da rainon yara sama da matar da ta fara girma, jikinta ya fara gajiya, kwakwalwarta ta fara tara matsaloli. Domin ita karama ko a bangaren mu’amula ta fi fahimtar yara, su ma sun fi fahimtarta, sama da wadda ta girma sosai, domin ta biyun ba ta cika iya jure wa shirmen yara ba wajen magana ko mu’amula. Sai a ga tana mu’amulantar kananan yara kamar wadansu manya.
Wannan zai sanya in tsallaka batun da ’yar uwa ta kawo na cewa matsalar aure da wuri da mata suke yi yana hana samun tarbiyya kamar yadda ta ce. Ina so in kulla alakar wannan zancen da kuma maganarmu ta baya. Idan mace ta zurfafa karatu domin samun ilimin da za ta dogara da shi, na san dai ko digiri na uku ne da ita a tsabar zurfafa karatu, babu wanda zai ba ta albashi, sai idan tana aikin gwamnati ko na kamfani ko banki da makamantansu. To abin da na ga ya fi faruwa shi ne, idan mace tana fita karatu ko aiki ko duk wata hidima da take tilasta mata barin gidanta na tsawon lokaci, idan tana da yara sai ta samo musu mai raino ko mai aikin gida tare da raino gaba daya. Ire-iren masu rainon nan yawancinsu kananan yara ne wadansu kasa da shekara goma, wadansu kuma sama da haka, kadan. A nan, da yaran da suke tare da mahaifiyarsu wadda ta san ciwonsu komai yarintarta da wadanda suke tare da yarinyar da ba ta san ciwonsu ba ita ma neman na kanta ne ya kawo ta gidansu, su wane ne tarbiyyarsu ta dan fi dama-dama?
Maimunatu Abba Wabi (Mrs)
[email protected] ailto:[email protected]
Za mu ci gaba