Matar Bahaushe Ko Mijin Bahaushiya? (3-4)

Na tabbata in aka yi haka, to kila abin da ya faru ga irin su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami da wasu da dama da bai same su ba a tsawon rayuwa. Aure bautar Ubangiji ne ya kamata ya zama Malam, ba BAUTA ba! A lokacin da na […]

Matar Bahaushe Ko Mijin Bahaushiya? (3-4)
Matar Bahaushe Ko Mijin Bahaushiya? (3-4)

Na tabbata in aka yi haka, to kila abin da ya faru ga irin su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami da wasu da dama da bai same su ba a tsawon rayuwa. Aure bautar Ubangiji ne ya kamata ya zama Malam, ba BAUTA ba!

A lokacin da na kawo kan wannan gaba na bayananta, abubuwa da dama suka shigo mani cikin rayuwa.

Na farko dai, bisa ga dukkan alamu wannan mata, mace ce mai son ganin ’yan uwanta mata sun samu damar da za su kasance cikakku daga cikin halitta, ko kuma su daga daga wani matsayi da suke, wanda take ganin bai ishe su ba, zuwa ga wani da take ganin shi ne mafi a’ala.

Na biyu, daga amon kalamanta kuma na fahimci cewa ta ga duniya ko dai ta zahiri ko ta makaranta, domin kuwa bayananta na nuna mani cewa tana da abubuwan fada game da rayuwar mata, kila har da misalai.

Na uku kuma shi ne, akwai wani abu da take son ta gaya mani, amma take noke-noke, ko tana tsoron irin yadda zan kalle ne ta bayan ta amaye.

Ganin cewa turakar da muke wannan zance tawa ce, ba kuma wanda ya san abin da ke wakana, daga ni sai ita, ba kuma wasu sharudda da aka gindaya game da abin da za mu fada wa juna, ya sa na koma baya domin tabbatar da ina muka nufa daga nan.

Zama na yi na tura mata sako cikin dare ina cewa, duk da ban san ko da wa nake zance ba, domin a bangon gidanki ba hoto, na shiga cikin dakin naki kuma ban ga wani jawabi da ya nuna mani ko ke wace ce ba, sa’annan ga shi ba ki bayyana ko ma macen ba ce ko namiji, amma na biye maki ne, a matsayin mace, ba don komi ba sai don fagen na ilimi ne, fage ne na karuwa da juna, daga namiji ko mace ko kuma daga wa ma! In kin lura ina dari-dari wajen amsa ki da fadada bayanai saboda rashin sanin tabbas, amma idan ba ki damu ba me zai hana a bayyana kai, sai mu yi keke da keke, don ban yarda da wasu bayanan naki ba.

Ba a ko dade ba ta maido da amsa, tana cewa ‘wallahi Malam ba dodorido nake maka ba, ina biye da kai da sauran abokai na facebook da dadewa. Ka san yadda lamurran suke ne, bayyana a fili na iya kawo matsala, gare ka ko ni, musamman ma ni. Kuma sai na ga bayyana kai bai karawa ko ragewa bisa ga ilmin da muke musaya. Ni fatata ita ce na karu, na kuma karar da kai da kuma dimbin dalibanka da ke biye da kai a kullum da kuma masoyanka a duniyar facebook, kila ta haka a samu canji a tunani ko zahiri game da yadda muke daukar lamurran karatu da ayyukan mata a wannan zamani. Dukkan abin da na fada da wanda zan karasa zuwa gobe in sha Allah, gaskiya ce ko dai daga zuciyata da karatuna da kuma abin da ya faru a zahiri. Wallahi Malam kana iya karaswa, ni a tawa fahimta, yawancin matan Hausawa ba bautar aure suke yi ba, bauta ce irin ta tsakanin wanda aka fi karfi a tsakanin ‘yan Adam.’

A cikin daren nan na koma farkon farawa a cikin akwatin sakona na kwashe dukkan abin da ta turo man da amsoshin da na ba ta, na zube a akwatin tattara bayanai na cikin kwamfutata domin tanadin gobe. Na san zan bukaci wadannan bayanai nan gaba.

Kammala haka ke da wuya sai na lalube ta, amma ban ji motsinta ba, na ce a raina kila ta yi barci, sai na tura sakon da ke cewa ‘wa ke bautar da matan da kike ikirari, me kuma ya faru ga su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami? Zan so na ji ko ma karu?’

A cikin kwanakin da muka yi muna tattaunawa, wannan shi ne karo na farko da na kosu da ganin amsar wannan baiwar Allah, domin kuwa da alama nan ne ruhin zancen nata yake, kuma ni ma ina da masaniyar cewa in da a fili ake wannan tattaunawa to da kila yanzu an yi mata caa, ganin cewa ba kowa ne ke jure tunani na kamfen din sa wa mata wata sabuwar rayuwa daga wadda suke ciki ba. Sa’annan batun inganta rayuwar mata a tsakanin Hausawa akan lullube shi da mahangai masu yawa da yawanci ba haka ya kamata su kasance ba.

Tun da safe na bude akwatin sakona, shiru. Ina ofis ina aiki, nakan leka ko akwai sakonta, ba labari. Can na kammala sallar la’asar, na shiga sai ga sakon nata, tana cewa; ‘A yi mani aikin gafara game da batutuwan da zan fada yanzu da kuma nan gaba. Na san za ka fahimta, ba turjiya da neman tashin-tashina ba ce, ni yadda na kalli lamurran ne. Tana yiwuwa ban kalle su da kyau ba, amma ina da yakinin abin da ke faruwa a cikin yawancin gidajen mazajen Hausawa dangane da mata ko addini bai amince da shi ba, ana dai shiga cikin rigar addini ne, amma da alama al’adu da son rai da daure gindin hukuma, su ne ke kara tabbatar da wannan matsayi da mata ke ciki. Addini cewa ya yi a yi aure domin a samu abubuwa guda uku.

Natsuwa tsakanin namiji da mace.

Samar da iyali da kuma kimtsa iyalin da tabbatar da iyalin bisa tafarkin da ya dace.

A samu haihuwa domin ci gaban gudanuwar al’umma da kuma kasancewa abin alfahari a ranar tashin kiyama.

Ta ci gaba cewa ‘Allah ya gafarta Malam ni a tawa fahimtar da nazarin da na yi, sai na ga kusan dukkan wadannan batutuwa uku da wasu irin su, a baibai ake gudanar da su a tsakanin Hausawa, musamman ta inda ya shafi mata.

Za mu Ci Gaba