Matar Bahaushe: Martani
Yau kamar yadda muka saba, mun zo muku da kadan daga cikin martanonin da kuka aiko game da rubutun da muka yi na MATAR BAHAUSHE. A sha karatu lafiya: Muhammad Mahmud:Gaskiya akwai abubuwan lura. Rayuwar Bahaushe tana bukatar gyara ta fuskoki da dama wallahi. Ni a koyaushe irin wadannan maganganun suka taso nakan ce wai […]
Yau kamar yadda muka saba, mun zo muku da kadan daga cikin martanonin da kuka aiko game da rubutun da muka yi na MATAR BAHAUSHE. A sha karatu lafiya:
Muhammad Mahmud:
Gaskiya akwai abubuwan lura. Rayuwar Bahaushe tana bukatar gyara ta fuskoki da dama wallahi. Ni a koyaushe irin wadannan maganganun suka taso nakan ce wai mene ne abin yi? Wayar da kai wani lokacin tasirinsa yana yin wuya idan wanda zai waye din shi yake amfana da yanayin da ake tattaunawa.
Umar A. Idris:
Idan mutum yana nazarin irin wadannan maganganu sai ya rasa ta ina za a fara? Kuma su wa za su jagoranci lamuran gyaran halin Bahaushe? Allah dai Ya kara basira har a kai mu tudun-mun-tsira.
Abdullahi Garba Jani:
Ai dama inda gizo ke sakar shi ne a gano matsalar, daga nan sai neman bakin zaren warware ta, to tunda Allah Ya sa an fara diga abin rubutu, to in sha Allahu za a yi wa tufkar hanci. Allah Ya saka.
Habiba Bamalli:
Allah Ka fidda Indo da A’i da Hajara da ma irinsu daga cikin wannan hali. Amma da alamu kamar yadda labarin ya nuna an kusa samun mafita insha Allah.
Muhammad Jamil Ibrahim:
Wannan shi ne abin da ke addabar al’ummar da muke ciki, musamman ta Hausawa. Akwai ire-irensu Halima da yawa, to amma abin tambaya a nan shi ne, zawarawan da ke auren Halima ba su san tana da tawagar yara ba ne kafin su aure ta? Wannan ya sa da yawa cikin mazan Hausawa matansu za su kai su wuta idan ba su tuba ba. Ya kamata a yi kira da babbar murya kan matsalolin aure ko a rage yawan mutuwar aure a Arewacin Najeriya.
Aliyu A. Wali:
Wallahi matsayin Halima da irinta ba za su lissafu ba a al’ummarmu!
Lawal Ibrahim Tanimu:
Amma masu nazari a kula da kyau, shin ana yin kokari wajen dabbaka abin da aka karanta, ko kuma me zai hana a kara yin kira ga su ma matan Hausawan, wajen ganin sun sauke nasu nauyin na yi wa mazan da’a daidai gwargwado ko kuwa su mata ba su da matsala sai maza?
Dauda Yahaya Ango Makarfi:
Matar Bahaushe gaskiya kam Halima an zalunce ki da iyayenki suka sanya miki rigar aure daga gama sanya rigar firamare.
Musa Fatima:
Ina rokon mazan Hausawa ku daure ku ba matan mu Hausawa rayuwar ci gaba don Allah, tunda Musuluci ya ba mata hakki, to ku jure ku ture maguzanci da danniya ku ba su hakkinsu daidai gwargwado
Auwal Badaru Faskari:
Mata an samu yadda ake so, na san yanzu baki na nan har kunne. Amma fa idan an bi ta barawo a dawo a bi ta ma bi sawu, domin kuwa idan dai har bera na da sata to daddawar nan fa ita ta ja wa kanta. Mata ne a sahun gaba wajen mayar da ’yan uwansu mata wani abu ba mutum ba, ba kuma dabba ba.
Sulaiman Aliyu Zango:
Uhhhm!!! Mijin Bahaushe mai ban haushi, duk da cewa ba ta yi bayanin irin tata-burzar da Maryam ta yi da mijinta ba a lokacin da guguwarsa ta karin auren ta taso, kafin Maryam ta samu kanta a gidan gado.
Saleh Zainab:
Mata Mutane. Allah Ya datar da mu, amin. Duk namijin da ya bar matarsa ta shekara ashirin sannan ya yi mata kishiya, ya cuce ta. Mata ku tambayi mazanjenku, in har suna da ra’ayin kara aure su yi da wuri ba sai girma ya fara kama ku ba a auro sa’ar ’ya’yanku.
Salisu Hapijo Haladu:
Tabdi jam…neman ilimi tilas ne kuma da ilimi ake gyara al’umma. Ashe ma mata na da wasu riguna daban-daban da matsayi daban- daban? Na yarda da ciwon mace na mace ne, amma a gidan aure dole su shawarta da magidanta domin samun maslaha da aminci. Muna jin dadin sauraronku kuma za mu ba ku goyon baya!
Muhammad Aminu Kabir:
Salam, bayan bibiya da na yi sai na ga kamar alamu na nuna cewa an tsallake MATAR BAHAUSHE kashi na uku ko kuma kila na hudu zai koma uku, na biyar ya koma hudu. Muna godiya, Allah Ya kara basira, amin.
Kujama Soofee:
Madalla, Allah dai Ya sassaka da alheri, Allah Ya sa Malam yana dawwana mana wadannan alherai don wata ran dole mu nema a rubuce mu karanta a tsanake.
Umma Rimaye:
Gaskiya auren wuri sam ba shi da illa, yanayin rayuwar ce ta yanzu sai a hankali. Allah dai Ya sa mu dace.