Matar Bahaushe: Martani 2
Wani fitaccen Malami Addinin Musulunci da ke Bunza a Jihar Kebbi, kuma tsohon limamin sojoji a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo ya ce talakawan Najeriya za su la’anci duk wadanda suke la’antar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan halin da ake ciki a kasar nan.Malam Abubakar Atiku ya bayyana haka […]
Wani fitaccen Malami Addinin Musulunci da ke Bunza a Jihar Kebbi, kuma tsohon limamin sojoji a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo ya ce talakawan Najeriya za su la’anci duk wadanda suke la’antar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan halin da ake ciki a kasar nan.
Malam Abubakar Atiku ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke garin Bunza, inda ya ce masu sukar gwamnatin Buhari ’yan adawa ne da masu hassada da kuma azzaluman ma’aikata da barayin gwamnati da suka sace dukiyar jama’ar kasar nan.
Ya ce irin wadannan mutane ne suke sukar wannan gwamnati suke la’antarta, suna cewa wai ana cikin wani mawuyacin hali a kasar nan, bayan sun san wadanda suka jefa kasar a cikin mawuyacin halin.
Shehin malamin ya ce a gwamnatin da ta gabata idan muka fito daga gidajenmu muna ganin kamar ba za mu iya komawa ba, saboda halin da ake ciki. Amma yanzu wannan tsoro ya kau sakamakon zuwan wannan gwamnati. “A baya noma da kiwon da muke yi a Arewa ’yan Boko Haram da barayin shanu duk sun hana, duk inda mutum zai je a firgice yake, duk ba mu ga wannan bala’i da Allah Ya kawar mana ba, shi ne ake cewa kasa ta shiga matsi? Shin matsin da muka shiga na kisa da ake yi mana a lokacin gwamnatin da ta gabata, amma yanzu an dakile hakan shi ne ake cewa an shiga matsi? Ko yau a cikin rediyo na ji ana cewa ’yan Boko Haram 800 sun ba da kai sun aje makamansu, ka ga wannan ba karamar nasara ba ce ga kasa,” inji malamin.
Ya kara da cewa: “Mu a nan Jihar Kebbi mun ga babban canji mai ma’ana domin kananan manomanmu ba su taba samun nasarar noman rani irin bana ba, saboda tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba su, jama’a sun samu makudan kudi a noman shinkafa. Saboda haka ina kira ga talakawan Najeriya, su gane cewa masu soke-soken suna yi ne don bata wannan gwamnati. Kuma ina kira ga ’yan Najeriya mu ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’o’in alheri mu yi wa watsi da masu soke-soken,” inji shi.