Matar da aka zarga da sayar da jaririnta a Suleja ta shiga hannu

Matar nan da Aminiya ta ba da labarinta ta sayar da jaririnta mai wata biyu a kauyyen Chaza da ke kusa da Suleja ta Jihar Neja da aka gano shi a Anacha Jihar Anambra ta shiga hannu, inda aka kama ta a garinsu Makurdi inda ta koma da nufin fara kasuwanci da kudin jarinin Naira […]

Matar da aka zarga da sayar da jaririnta a Suleja ta shiga hannu
Matar da aka zarga da sayar da jaririnta a Suleja ta shiga hannu

Matar nan da Aminiya ta ba da labarinta ta sayar da jaririnta mai wata biyu a kauyyen Chaza da ke kusa da Suleja ta Jihar Neja da aka gano shi a Anacha Jihar Anambra ta shiga hannu, inda aka kama ta a garinsu Makurdi inda ta koma da nufin fara kasuwanci da kudin jarinin Naira dubu 150.
Babban Jami’in ’Yan sanda na “B” Dibision da ke Suleja, wanda ya tabbatar da kamata ga Aminiya, ya ce ’yan sandan Jihar Benuwai suka je kauyen Chaza, inda suka gayyaci wani mai suna Mista Francis Baba Amala da ke ikirarin ya amshi jaririn daga wurinta bisa dalilan jinkai, ya ba da shi ga wata ’yar uwarsa da ke Anacha Jihar Anambra da Allah bai ba ta haihuwa ba don renonsa. Ya ce an kama wata mai suna Hebilin da ake zargi da taimakawa wajen harkar, inda aka kai su Makurdi, bayan an sanar da ofishinsu abin da ke tafe da su.
A zantawarta da wakilinmu bayan dawowarta, Hebilin ta ce, ta sanar da ’yan sanda alakarta da uwar jaririn, wadda a cewarta ta zauna da ita a kauyen Chaza na dan wani lokaci, kuma ba ta tashi sanin ta sayar da jaririn ba, sai bayan da ta bar kauyen inda ta wuce da yayar jaririn mai shekara uku.
Ta ce tuni an mika jaririn ga wata cibiyar rainon yara a Makurdi.  Ta ce, kudin da ake zargin na cinikin jaririn ne, an mayar mata su, sai dai an yi mata gargadin ta yi nesa da jaririn, inda ta ce ’yan sanda sun wanke su daga zargin hannu a cikin lamarin