Ba ta yi barci ba a shekara 30

Ba a haka aka haife ta da halittar rashin barci ba, ita ta tsara wa kanta don makara daga barci tun tana yarinya.

Ba ta yi barci ba a shekara 30

Ana yi wa wata mace mai suna Nguyen Ngoc My Kim mai ’yar ƙasar Vietnam laƙabi da “mai halittar rashin barci” saboda zargin ba ta yin barci gaba ɗaya.

Nguyen mai shekaru 49 ta yi da’awar cewa ba ta yi barci ba a tsawon shekara 30 da suka gabata.

Labarin Nguyen wacce tela ce a Lardin Long An, ya ɗauki hankali ne bayan da ta tabbatar wa kafofin yaɗa labarai cewa ba ta yi barci ba tsawon shekaru da dama, kuma rashin barci gaba ɗaya bai shafi lafiyarta ba.

Duk da haka, Misis Kin, kamar yadda wasu ke kiran ta, ta ce ba a haka aka haife ta da halittar rashin barci ba, ita ta tsara wa kanta daga makara yin barci tun tana yarinya.

Ta ce da farko takan rasa isasshen barci domin tana son karatu zuwa dare, daga baya kuma idan ta fara ɗinki sai ta daɗe tana yi don ta cika alƙawarin abokan hulɗarta.

Misis Kim ta ce a wani lokaci, ba ta jin barcin kwata-kwata, don haka ba ta yi.

“Duk dare haka nake, nakan zauna a gaban keken ɗinkina, ba na yin barci, domin ina tsoron rashin cika alkawari,” in ji Nguyen Ngoc My Kim ga wa manema labarai.

“Lokaci na farko da na yi aiki cikin dare na fuskanci matsaloli da yawa.

“Ba na yin barci a kullum kuma nakan yi kura-kurai da yawa idan ina yin ɗinki, amma a koyaushe ina jin gajiya da ɗimuwa, har ma na taɓa samun haɗarin mota.

“Duk da haka, bayan na fuskanci rashin barci na tsawon watanni, da shekaru da yawa, idanuna da jikina sun saba da rashin barci. Tun daga nan, ba na iya yin barci ba ko da ina so,” in ji Kim.

Har yanzu ba a tantance dalilin hakan a likitanci ba, amma ta yi ikirarin cewa galibi mutane suna ganin ta tana aiki dare da rana, domin koyaushe tana wajen ɗinkinta a unguwar Long Cang commune, Long An.

Ta ce a kodayaushe kofarta a buɗe take, don haka mutane za su iya shiga kawai ko su kalli aikinta idan sun ga dama.

“Da farko, mutane kaɗan ne suke kula da rashin barcina, amma daga baya, da yawa daga cikinsu sun fara lura cewa koyaushe ina wajen aiki.

“Shi me suka yaɗa labarin, kuma nan da nan na zama sananniya saboda halittar da nake da ita ta kasancewa mai rashin barci,” in ji ta.

Labarin cewa Miss Kim ba ta yi barci ba cikin shekara 30 kwanan nan ya yaɗu a shafukan sada zumunta na Vietnam.

Sakamakon hakan mutane baƙi daga sassan kasar suka riƙa zuwa domin gane wa idanunsa gaskiya ce.