Matar da likitoci suka manta almakashi a cikinta tsawon shekara biyar

Ba zan iya kwatanta irin zafin da na ji tsawon shekara biyar.

Matar da likitoci suka manta almakashi a cikinta tsawon shekara biyar

Likitoci a kasar Indiya sun manta da almakashi a cikin wata mata bayan sun yi mata tiyata bisa rashin sani.

Matar mai suna KK Harshina mai shekara 31 daga Jihar Kerela ta je asibiti ne bisa larurar haihuwa inda aka yi mata aiki, amma bayan gama aikin cikin nasara ta kuma tafi gida, sai ta rika fama da matsanancin ciwon ciki.

“Da na bayyan irin matsanancin zafin da nake ji ne, sai likitocin asibitin suka ce min ina jin zafin ne saboda aikin da aka yi min wanda shi ne karo na uku, kuma da dama sun kai irin wannan kukan,” in ji Harshina.

Hakan bai sa ta hakura ba, bayan da zafin ya tsananta na tsawon lokaci, da ya sa ta tafi wajen wasu likitoci a inda ba a gano matsalar ba, sai dai bayan da aka yi hoton cikin aka gano almakashi na tiyatar da aka yi mata ne a baya.

“Ba zan iya kwatanta irin zafin da na ji tsawon shekara biyar (da wannan almakashi a cikina) ba,” in ji matar a hirarsu da wakilin BBC, Imran Kuriesh wanda ya tattauna da ita a fafutikar da take yi ta neman diyya da kuma hukunta likitocin da suka yi mata aikin.

An yi wa Harshina wadda take da ’ya’ya uku tiyata ce, domin ciro jariran, inda aka yi mata aiki a Asibitin Koyarwa na Makarantar Koyon Aikin Likita ta Gwamnati a inda aka ciro namiji a shekarar 2017.

Duk da cewa Harshina Musulma ce, ta samu goyon bayan matan kasar daga addinai daban-daban don ganin an hukunta wadanda suka yi wannan sakaci da nuna rashin kwarewa domin a yi wa tufkar hanci.