Matar da mijinta ya buya a ban-daki saboda ’yan fashi ta bukaci a raba aurensu

Matar ta yi korafin cewa mijin nata ragon maza ne

Matar da mijinta ya buya a ban-daki saboda ’yan fashi ta bukaci a raba aurensu

Kotu

Wata mata ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta, Abidemi da ya gudu ya buya a ban-daki lokacin da ’yan fashi suka shigar musu gida, inda tace ragon maza ne.

Matar, wacce ’yar kasuwa ce mai suna Asiata Oladejo, ta shigar da wannan koke ne ranar Laraba a kotun Mapo da ke Ibadan a jihar Oyo.

Asiata ta ci gaba da sanar da kotun yadda ta shiga tsananin kaduwa lokacin da ’yan fashin suka shigar musu gida, kuma mijin nata ya hango su ya shige ban-daki ya bar ta da yaran su uku ’yan fashin su yi yadda suka ga dama da su.

“Ya mai shari’a, lokacin da barayin suka shigo da karfe 1:00 na dare na nemi mijina na rasa, sai ni da ’ya’yanmu kawai, sai da suka tafi sannan muka gan shi ya fito daga ban-daki,” inji ta.

Ta kuma ce ta sha rokonsa kan ya karbo musu hayar wani gidan amma ya ki, sannan kuma yana da dan karen neman mata.

To sai dai mijin nata ya roki kotun ta tausaya masa domin kuwa matar tasa fada ne da ita duk da kasancewarta tela, haka kawai sai ta je wurin sana’arsa ta yi masa tijara.

“Da gaske ne na buya a ban-daki lokacin da ’yan fashi suka shigo. Amma bayan nan ba yadda ban yi da ita ta dawo gida ba da ta tafi amma ta ki wai kawai saboda ta tsorata,” inji mijin.

A karshe ya roki kotun ta bar masa rikon ’ya’yan nasu, saboda kowa ya san shi namiji ne mai kula da iyalinsa.

Alkalin kotun, S. M. Akintayo ta ba wa matar tasa umarnin dakatar da duk wata barazana ko cin zarfi, ko katsa-landan a harkarsa, sai dai ta hana shi rikon ’ya’yan.

Ta ce hakan ya biyo bayan duba da cewa Asiata za ta fi shi kula da su, kodayake ta ce su biyu za su dauki nauyin karatu da kula da su.

Sannan Alkalin ta ce Abidemi zai dinga biyan N20,000 duk wata don kula da yaran.

Kan batun raba auren kuwa, ta ce dama auren na su bai cika dokar yin aure a Najeriya ba, don haka babu shi.