Matar da ta fara ginin gida har ta kammala ita kadai
Hotunan wata mata ’yar asalin kasar Afirka ta Kudu sun karade gari bayan da aka gan ta ita kadai tana gina gidan da za ta zauna a ciki. Matar mai suna Zama Philisiwe Zungu mai kimanin shekara 26 ta zama wata shaida da aka rika amfani da ita a bikin Ranar Mata da aka yi […]
Hotunan wata mata ’yar asalin kasar Afirka ta Kudu sun karade gari bayan da aka gan ta ita kadai tana gina gidan da za ta zauna a ciki.
Matar mai suna Zama Philisiwe Zungu mai kimanin shekara 26 ta zama wata shaida da aka rika amfani da ita a bikin Ranar Mata da aka yi a kasar saboda yin aikin da ake gani galibi maza ne suka fi shahara a kai.
A cikin hotunan da suka karade gari a kafafen sada zumunta, an ga Misis Zama tana aikin ginin ita kadai, tana kwaba siminti, jera bululluka da sauran ayyuka duk ita kadai.
Mutane da dama dai a kasar sun yi ta yaba wa jajircewarta inda suka ce za ta zama wata alamar karfafawa mata gwiwa.
Rahotanni sun nuna cewa Misis Zama kwararriyar injiniyar gine-gine ce kuma ta fara sha’awar aikin ne daga mahaifinta wanda sima maginin ne.
Ta yi karatunta ne a kwalejin TVET da ke garinta na Umgungundlovu bayan ta yanke shawarar fara karatun a shekarar 2014.
Zama a yayin wata tattaunawa da wata kafar yada labarai a kasar ta ce ba ta taba aiki a wani kamfanin gine-gine ba, kawai karatunta ne na makaranta ya ba ta kwarin gwiwar cewa za ta iya ginin da kanta.
Ta ce, “Wannan ne abin da na fi iyawa. Ginin gidana yakan ba ni nishadi yana kuma kayatar da ni, yin abu a zahiri ya fi koyonsa a baki.
“Ina da burin ganin na kafa kamfanin gini nawa na kaina saboda in samar wa mata ayyukan yi.
“A kodayaushe mutum sai ya zage damtse kuma ya yarda cewa zai iya yin abu da kansa ta hanyar jarrabawa”, inji Zama.