Matar da ta sace yarinya a coci ta shiga hannu

Wata mata mai suna Anuoluwapo Joshua ’yar shekara 28 ta shiga komar ’yan sanda bayan kimanin wata 6 da rundunar ke nemanta saboda ta sace yarinya ’yar shekara uku mai suna Akamaka Patience, a wani babban coci da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi […]

Matar da ta sace yarinya a coci ta shiga hannu

Wata mata mai suna Anuoluwapo Joshua ’yar shekara 28 ta shiga komar ’yan sanda bayan kimanin wata 6 da rundunar ke nemanta saboda ta sace yarinya ’yar shekara uku mai suna Akamaka Patience, a wani babban coci da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa tun a watan 7 na shakarar 2017 wacce ake zargin ta sace yarinyar a cocin. “Mahaifiyar yarinyar ta bar ’yarta a inda ake yin addu’a ne sai ta je ɗakin ajiyar kayayyaki da nufin ɗebo wa yarinyar kayanta. Koda ta dawo ɗakin bautar sai b ata ga ’yar tata ba. Nan aka yi ta nema amma ba a dace ba, inda a lokacin iyayen yarinyar suka shigar da kokensu ga rundunar ’yan sanda. Dubun wacce ake zargin ta cika ne a ranar juma’ar makon jiya, bayan da aka ga yarinyar a cocin da aka sace ta tun da fari,” inji shi.

Dubun Anuoluwapo ta cika ne bayan da ta je da yarinyar cocin da ta sace ta tun da fari, a lokacin da cocin ta shirya addu’ar ƙarshen shekarar 2017 ga yara ƙanana, sai iyayen yarinyar na asali suka ganta a cikin taron yara. Nan take suka sanar da ’yan sandan yankin, waɗanda suka zuba ido har bayan da aka ƙare shirin yi wa yaran addu’ar; sai da wacce ake zargin ta ƙaraso ta kama hannun yarinyar da nufin tafiya da ita, nan take jami’an ’yan sandan suka cafke ta.

Wacce ake zargin ta shaida cewa tun da fari ta faɗa wa saurayinta cewa tana ɗauke da cikin da yayi mata, bayan wani lokaci sai ta yi tafiya zuwa Arewacin ƙasar nan, bayan da ta dawo ne saurayin nata ya matsa mata da tambayar labarin ’yarsu, sai ta faɗa masa cewa za ta je Jihar Nasarawa a Arewa ta ɗauko ta. A maimakon haka sai ta garzaya cocin ta sato yarinyar, inda ta kai wa saurayin nata, suka kuma ci gaba da ba ta kulawa.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin sashin binciken manyyan laifuka su ci gaba da bincikarta, kafin ta gurfana a gaban kotu.