Matar da ta yi aure 10 a kasa da shekara biyu ta shiga hannu a Iran

Wata mata ’yar kasar Iran ta shiga hannun hukuma, inda ake tuhumarta da yin aure har sau 10, ta kuma rabu da mazajen nata, al’amarin da ya wakana cikin kasa da shekara biyu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito. Wadda ake tuhuma da yaudarar mazan, dokokin shari’ar Musulunci sun kamata da yaudara […]

Matar da ta yi aure 10 a kasa da shekara biyu ta shiga hannu a Iran
Matar da ta yi aure 10 a kasa da shekara biyu ta shiga hannu a Iran

Wata mata ’yar kasar Iran ta shiga hannun hukuma, inda ake tuhumarta da yin aure har sau 10, ta kuma rabu da mazajen nata, al’amarin da ya wakana cikin kasa da shekara biyu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.

Wadda ake tuhuma da yaudarar mazan, dokokin shari’ar Musulunci sun kamata da yaudara don ta samu rabin sadakinta a mafi yawan lokutan domin ba ta tarawa da mazan.
A al’adar kasar Iran kuwa, matar da za a aura ita ke yanka wa kanta sadaki, inda ango ke biya a sulallan zinari.
Ita kuwa wannan matawshiya, ’yar sehekara 20, ta karyata tuhumar da ake yi mata, inda ta ce ta auri mazan ne, amma nan take ta bukaci su biyata sadakinta, kuma ba tare da sun tara da ita ba, kamar yadda wata jaridar kasar Iran ta ruwaito.
Mazajen da ta aura duk sai da suka ba ta rabin sadakin saboda gudun kada su saba wa doka, amma sai matar ta ce ai yarjejeniyar da suka kulla ita ce, za a ba ta sulallan zinari 100 zuwa 110, wato a tsarin doka wannan ya yi kasa da abin da ya kamata a biyata.
Wannan mata dai ta yi ta tursasa mazajenta har sai sun saketa. Matar da aka saketa a kasar Iran ta kan cire sunan mijinta na da daga katin dan kasa. Ita kuwa wannan mata ta sha yin haka, al’amarin da ya ba ta dama wajen cutar mazajen da ba su santa ba.
“Ban ga dalilin da ya sa zan amsa wadannan tambayoyi ba,” a cewarta, lokacin da mai bincike a kotu ya kirawo daukacin mazaje 10 da ta aura.
“Ba ni da wani laifi. daukacin aure-auren da na yi ba su saba wa doka ba; daukacin mazajen da na aura sun yi auren ne a kasahin kansu, mun kuma rabu ne saboda sabanin ra’ayi,” inji ta.
Kotu dai ta yanke tuhumarta da aikata zamba cikin aminci, wajen yin aure-aure, duk da cewa ba a fitar da ranar da za a yanke mta hukunci ba.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume