Matar da ’yan sanda suka kama ta yi nadamar gallaza wa danta
Matar nan mai suna Blessing Goodluck, wacce ’yan sanda suka kama a karshen makon da ya gabata kan zargin azabtar da danta mai shekara tara a duniya mai suna Kingsley kuma ta jefar da shi a wani gidan mai da ke Ijaye a yankin Agbado da ke Jihar Legas, ta ce ta yi da-na-sanin danyen […]
Matar nan mai suna Blessing Goodluck, wacce ’yan sanda suka kama a karshen makon da ya gabata kan zargin azabtar da danta mai shekara tara a duniya mai suna Kingsley kuma ta jefar da shi a wani gidan mai da ke Ijaye a yankin Agbado da ke Jihar Legas, ta ce ta yi da-na-sanin danyen hukuncin da ta yi wa danta.
Blessing Goodluck ta bayyana cewa ta yi nadamar abin da ta aikata kuma ba za ta sake ba nan gaba.
“Na yi da-na-sanin abin da na yi. Na wuce gona da iri. dana Kingsley ba ya jin magana kuma yaro ne mai yawan tsokana. Ba ya zama a gida sai ya rika bin gidajen jama’a yana jawo mani magana, sai ni kuma da na gaji na dauki mataki amma na yi alkawarin ba zan sake ba, na koyi darasi,” inji ta.
To sai dai mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas, Kanneth Nwosu, ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da ita a gaban shari’a don ya zama darasi ga jama’a.
Ya ce: “Abin da Blessing ta yi ya saba wa doka kuma cin zarafin yara ne. Mun kama ta a kan titin Sule Babalola da ke Unguwar Agbado. Ta bar yaron a cikin wani hali har sai da aka kai shi asibitin gwamnati da ke Unguwar Ile Epo. Saboda haka doka ba za ta bar ta ba.”
Aminiya ta gano cewa Blessing ’yar kimanin shekaru 23 a duniya ta yi wa danta Kingsley dukan kawo wuka har ta yi masa rauni a jiki da tsumangiya saboda ya gaida wani makwabcinsu da ba ta shiri da shi.
Bincike ya nuna cewa tun ranar daya ga watan nan ne mahaifiyar Kingsley ta ajiye shi a wani gidan mai da ke Unguwar Agbado ta yi tafiyarta ta bar shi yana ta sheka kuka.
Wadansu mutanen kirki ne suka tausaya wa yaron, suka rika ba shi abinci sannan daga bisani suka kai shi ofishin ’yan sanda da ke Unguwar Ijaiye-Ojokoro.
Yaron dan aji biyu a makarantar firamare, an kai shi asibitin gwamnati don a duba lafiyarsa sannan daga bisani aka ajiye shi a ofishin rundunar ’yan sandan Jihar Legas.
Aminuya ta gano cewa ’yan sanda sun bi sawun Blessing har unguwar Ojuelegba, inda yaron ya yi ikirarin a nan suke zaune amma duk da haka ba su same ta ba.
Sai daga bisani da suka tsananta bincike suka kamo ta a Unguwar Agbado da ke Jihar Legas, inda ta buya don kauce wa kamu.