Matar da ‘ya’yanta 7 cikin 8 suka rasu ta ce tana cikin matsala

Wata mata da ’ya’yanta suke mutuwa a kai-a kai, har ’ya’yanta bakwai daga cikin takwas suka rasu, ta koka ganin na karshe ya fara ciwo. Matar wadda yanzu take jinya a Babban Asibitin kasa a Abuja, ta ce ’ya’yanta suna yawan mutuwa. Wani mai taimakon al’umma, Uche Onyemobi wanda ya kai dauki ga matar a […]

Matar da ‘ya’yanta 7 cikin 8 suka rasu ta ce tana cikin matsala

Wata mata da ’ya’yanta suke mutuwa a kai-a kai, har ’ya’yanta bakwai daga cikin takwas suka rasu, ta koka ganin na karshe ya fara ciwo.

Matar wadda yanzu take jinya a Babban Asibitin kasa a Abuja, ta ce ’ya’yanta suna yawan mutuwa.

Wani mai taimakon al’umma, Uche Onyemobi wanda ya kai dauki ga matar a asibiti, ya tabbatar da cewa tana da ’ya’ya takwas, kuma ta rasa bakwai daga cikinsu, kuma yanzu haka tana jinyar na takwas din ne a asibiti.

Matar wadda take tare da ’yarta a asibitin, tana addu’ar ganin ’yarta ta karshe ta rayu, kuma tana fatan ’yar ce ta za binne ta, ba ita za ta binne ’yar ba.

Ita dai marar lafiyar mai suna Ogechi Stella Njoku, tana cikin mawuyacin hali a yanzu haka, kuma har zuwa yanzu ba a yi mata aiki ba.