Matar Dabid Beckham za ta kai ziyara Ghana

Matar shahararren dan kwallon Ingila Dabid Bekcham mai suna bictoria za ta kai ziyara kasar Ghana.  Za ta ziyarci kasar ce a wani shiri na yaki da cutar kanjamau (HIb/AIDS) da sashen yaki da cututtuka na Majalisar dinkin Duniya ya shirya.Matar wacce shahararriyar mawakiya ce, majalisar dinkin duniya ta zabo ta ne a matsayin Jakadar […]

Matar Dabid Beckham za ta kai ziyara Ghana
Matar Dabid Beckham za ta kai ziyara Ghana

Matar shahararren dan kwallon Ingila Dabid Bekcham mai suna bictoria za ta kai ziyara kasar Ghana.  Za ta ziyarci kasar ce a wani shiri na yaki da cutar kanjamau (HIb/AIDS) da sashen yaki da cututtuka na Majalisar dinkin Duniya ya shirya.
Matar wacce shahararriyar mawakiya ce, majalisar dinkin duniya ta zabo ta ne a matsayin Jakadar majalisar na yaki da cutar kanjamau a sassan duniya.
Mista Gimay Haile, Daraktan da ke kula da yaki da cutar a Ghana ne ya sanar da ziyarar mawakiyar a lokacin da yake gabatar da wani shiri a talabijin kasar.
A shekarar 2004 ce Majalisar dinkin Duniya ta zabi bictoria a matsayin Jakadiyar yaki da cutar kanjamau a sassan duniya.  Ana sa ran za ta gana da mata da kuma kananan yara da suka kamu da cutar don fadakar da su hanyoyin da yakamata su bi cigaba da rayuwa a yayin ziyarar.
Shekaru da dama bictoria Beckham take shiga harkokin tallafa wa al’umma musamman gajiyayyu da kuma kananan yara kuma tana da sha’awar bayar da tallafi don ganin an yaki cutar kanjamau (HIb/AIDS) a sassan duniya musamman ma a yankin Afirka.