Matar El-Rufai ga Tinubu: Mijina bai cancanci wannan azabtarwa ba

Idan El-Rufai ya aikata laifi kotu ce za ta yanke hukunci, idan kuma ba shi da laifi, kotu ce za ta wanke shi.

Matar El-Rufai ga Tinubu: Mijina bai cancanci wannan azabtarwa ba

Matar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Asiya El-Rufai, ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar an bai wa mijinta haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada, tana mai cewa bai cancanci irin wannan azabtarwar ba.

Asiya ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani kan kama likitan mijinta na musamman, Farfesa Bello Abubakar, wanda Hukumar ICPC ta tabbatar da kama shi.

Da take magana da manema labarai a Abuja tare da matar El-Rufai ta biyu, Aichatou, ta ce ba sa neman Shugaban Ƙasa ya tsoma baki a shari’ar mijinta ko ya hana a gurfanar da shi, sai dai a ba shi damar samun kulawar likita, ganawa da iyalansa da lauyoyinsa, tare da ba shi beli cikin sharuɗan da zai iya cikawa.

Ta yi zargin cewa El-Rufai, wanda ta ce yana fama da hawan jini da ciwon sukari, an hana shi ganin likitansa na musamman, lamarin da ta ce ya jefa su cikin fargaba da damuwa.

Asiya ta tuna irin rawar da mijinta ya taka wajen yaƙin neman zaɓen Tinubu a 2023, tana cewa: “Mun tsaya tare da kai. Shin wannan ne sakamakon da iyalinmu suka cancanta?”

Ta kuma ce idan El-Rufai ya aikata laifi kotu ce za ta yanke hukunci, idan kuma ba shi da laifi, kotu ce za ta wanke shi, amma a halin yanzu ya kamata a ba shi duk haƙƙoƙin da doka ta tanadar masa.