Shin matar El-Rufai na so a ba mace Sarautar Zazzau ne?

Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai, ta yi barkwanci game da ko mijinta zai nada mace a matsayin wadda za ta jagoranci Masarautar Zazzau bayan rasuwar Sarki Shehu Idris. Cikin wani sakon raha da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Juma’a 25 ga watan Satumba, Hadiza El-Rufai, ta yi tambaya ko hakan […]

Shin matar El-Rufai na so a ba mace Sarautar Zazzau ne?

El-Rufai da Hadiza

Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai, ta yi barkwanci game da ko mijinta zai nada mace a matsayin wadda za ta jagoranci Masarautar Zazzau bayan rasuwar Sarki Shehu Idris.

Cikin wani sakon raha da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Juma’a 25 ga watan Satumba, Hadiza El-Rufai, ta yi tambaya ko hakan zai zai iya kawo daidaito tsakanin maza da mata.

“Bisa la’akari da batun tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, shin akwai yiwuwar a sake samun wata sarauniya a Masarautar Zazzau makamanciyar Sarauniya Amina?”

Aminiya ta ruwaito cewa masu zaben Sarki na Masarautar Zazzau sun riga sun fara aikinsu na zaben sabon Sarkin Zazzau kamar yadda al’ada ta tana da.

Kebewar tasu na zuwa ne tun a washegarin ranar rasuwar Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 bayan ya shafe shekara 45 a gadon sarauta.

Masu zaben Sarki a Masarautar Zazzau sun hada da Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu; Fagacin Zazzau, Umar Mohammed; Makama Karami, Mahmood Abbas; Limamin Juma’a, Dalhat Kasim; da kuma Limamin Kona, Sani Aliyu.

Bayan kammala aikinsu, masu zaben sarkin za su mika sunayen wadanda suka zaba ga Gwamnatin Jihar Kaduna domin bayyana wanda Allah Ya ba wa.