Matar Gwamnan Akwa Ibom ta rasu

Fasto Patience Umo Eno ta rasu a asibiti a sakamakon rashin lafiya

Matar Gwamnan Akwa Ibom ta rasu

Uwargidan Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, Fasto Patience Umo Eno, ta rasu.

Matar Gwamna Umo Eno ta rasu ne a asibiti a yayin da ake jinyar ta sakamakon rashin lafiya.

Gwamna Umo ne ya sanar da rasuwar mai ɗakin tasa ne kafin wayewar garin ranar Juma’a.

Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Ini Ememobong, a cikin sanarwar da ya fitar a safiyar Juma’a ya ce Fasto Patience ta rasu ne a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa duk da rasuwar, gwamnan yanba wa al’ummar jihar cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen hidima wa al’umma.

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri

Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa