Matar Gwamnan Kano na farko, Audu Bako, ta rasu

Ta rasu tana da shekara 93 a duniya, bayan ta sha fama da rashin lafiya.

Matar Gwamnan Kano na farko, Audu Bako, ta rasu

Hajiya Ladi Audu Bako, matar Gwamnan Jihar Kano na farko, Audu Bako ta rasu 

Ta rasu ne a ranar Laraba tana da shekara 93 bayan ta sha fama da rashin lafiya a asibitin ‘Prime Specialist’ da ke Kano.

Aminiya ta tattaro cewa za a yi jana’izarta a Masallacin Malam Inuwa Dutse da ke unguwar Sallari bayan Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da misalin karfe 1:30 na rana.

Audu Bako dan sandan Najeriya ne kuma gwamnan Jihar Kano na farko a lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon bayan an kafa jihar daga yankin Arewa.