Matar Gwamnan Kebbi ta jagoranci tattakin kariya daga Cutar Sankara
A ranar Asabar da ta gabata ce matar Gwamnan Jihar Kebbi kuma Shugabar Cibiyar Kula da Masu Cutar Sankara ta ‘Medicaid Cancer Foundation’ (MCF), Dokta Zainab Shinkafi Bagudu ta jagoranci wata tattaki na kilomita 5 a Abuja. A yayin tattakin na mutum miliyan daya na shekara-shekara, Dokta Zainab Bagudu, ta bayyana cewa baya ga motsa […]
Dokta Zainab Bagudu da sauran jama’a a yayin tattakin
A ranar Asabar da ta gabata ce matar Gwamnan Jihar Kebbi kuma Shugabar Cibiyar Kula da Masu Cutar Sankara ta ‘Medicaid Cancer Foundation’ (MCF), Dokta Zainab Shinkafi Bagudu ta jagoranci wata tattaki na kilomita 5 a Abuja.
A yayin tattakin na mutum miliyan daya na shekara-shekara, Dokta Zainab Bagudu, ta bayyana cewa baya ga motsa jiki, tattakin ya kunshi kara wayar da kan al’umma game da illar cutar sankara da kuma samar da mafita ga wadanda suka kamu da cutar.
Dokta Bagudu ta ce tattakin ya samu amincewar Hukumar Al’adu da Yawon Bude Ido ta Kasa, tana mai cewa yanayin da jama’a masu yawa irin wannan suka fito, yana kara sanya wa sauran al’umma sha’awar kwaikwayon wannan dabi’a da motsa jiki don kaucewa kamuwa da cutuka masu yawa.
“Muna fatan samun nasara daga Cutar Sankara. Muna fatan tattake cutar baki daya. Kuma a wannan karon mun samu mutane har daga Kasar Portugal wadanda muke wannan tattaki tare da su a bana.
“Za mu iya rage yaduwar cutar sankara fiye da rabi ta hanyar wayar da kan al’umma don cimma hasashen da duniya ke yi da kashi 25 cikin 100 kafin nan da shekarar 2025. Mun tara kudi Naira Miliyan 40 a bara, muna fatan samar da fiye da haka a bana, don tunkarar masu dauke da wannan cuta su samu waraka. Don haka ina karfafa wa jama’a gwiwar cewa mu ci gaba da yin tattaki,” a cewarta.
Ta kuma kara da cewa, “Daga wannan gangami, a yanzu zamu rage farashin tantancewa da kuma maganin cutar. Hakika jinyar Sankara ba abu ne mai sauki ba saboda munin cutar. Ana bukatar kudi masu yawa wajen yakarta, kuma dole a sanya makudan kudi cikin jinyar. Saboda haka muke tara kudade ta hanyar tilasta wa kanmu bada wani abu. Sannan muna nema a wajen gwamnati da sauran hukumomi.”
Haka zalika shugabar cibiyar ta Medicaid, ta ce cibiyar ta fadada ayyukanta wajen yin amfani da makarantun lafiya, don ilmantar da daliban Sakandare game da hadarin cutar Sankara da kuma Sikila; Da kuma shigo da Sarakunan Gargajiya wajen wayar da kan al’umma kan yaki da cutar ta Sankara da kuam tarukan shekara-shekara don inganta harkokin wanzuwar masu dauke da cutar.
Matar gwamnan ta ce a yanzu haka tana yin wani gagarumin shiri don bude rassa wannan cibiya a kowane yanki cikin yankunan Najeriya shida da ake da su a fadin kasar nan baki daya domin sanya dukkan gwamnatoci cikin wannan fafutika don kawo karshen wannan cuta a kasar nan.