Matar Gwamnan Kebbi ta shawarci mata su nemi ilimi

Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Hajiya Zainab Abubakar Atiku Bagudu ta shawarci mata su tashi tsaye wajen neman ilimi domin su taimaka wa mazansu, kuma su samar da kyakkyawar tarbiyya ga ’ya’yansu. Kakakin matar Gwamnan Hajiya Binta Abdulhamid ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Birnin Kebbi.Matar Gwamnan ta nuna […]

Matar Gwamnan Kebbi ta shawarci mata su nemi ilimi
Matar Gwamnan Kebbi ta shawarci mata su nemi ilimi

Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Hajiya Zainab Abubakar Atiku Bagudu ta shawarci mata su tashi tsaye wajen neman ilimi domin su taimaka wa mazansu, kuma su samar da kyakkyawar tarbiyya ga ’ya’yansu.

Kakakin matar Gwamnan Hajiya Binta Abdulhamid ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Birnin Kebbi.
Matar Gwamnan ta nuna cewa lokaci ya wuce da mata za su zura wa mazansu ido su biya musu dukkan bukatu da na ’ya’yansu musamman a wannan lokaci da ake ciki na rashin kudi.
Dokta Zainab Bagudu ta kuma bukaci mata su hada kai da mazansu don samun gagarumar nasara a harkokinsu na rayuwa.
Sai ta shawarci iyaye maza su kasance masu kula da tarbiyyar ’ya’yansu tare da sanya su a makaranta ta yadda za su kaurace wa shiga cikin miyagun halaye da za su sanya iyaye cikin halin kaka-ni-ka yi.
Dokta Hajiya Zainab Atiku Bagudu, ta yi nuni game da irin rawar da mata ke takawa wajen tarbiyyantar da iyali, inda ta ce amma hakan ba zai samu nasara sai da hadin kan maza a matsayinsu na jagororin iyali.
Dokta Zainab Bagudu ta yi kira ga mata masu ilimin zamani su rika karantar fannin aikin asibiti domin taimaka wa ’yan uwansu mata musamman a fannin haihuwa da sauran cututtukan da suke addabar mata, maimakon a ce maza likitoci ne ke duba wadanda ba muharramansu ba.
Ta ce duk inda ake da gibi a bangaren kiwon lafiya za su yi kokari su taimaka wa mata wajen karatun aikin lafiya.