Matar mai wakar ‘Najeriya Jaga-Jaga’ ta ba da kodarta an dasa masa

An yi wa wanda ya yi wakar Najeriya Jaga-Jaga dashen kodar matarsa a Najeriya

Matar mai wakar ‘Najeriya Jaga-Jaga’ ta ba da kodarta an dasa masa

(Hoto: Instagram/abdulkareemeedris)

Fitaccen mawaki Eeddris Abdulkareem, wanda ya yi wakar ‘Najeriya Jaga-Jaga’ ya gode wa matarsa Yetunde, bisa bayar da kodarta da ta yi aka dasa masa.

Mawakin ya bayyana hakan ne bayan ya fara murmurewa bayan an kammala aikin dashen kodar da aka yi masa.

Ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Ina godiya ga ta musamman ga Ubangiji bisa dashen kodar da aka yin min a karshen mako cikin nasara.

“Kalmomi ba za su iya bayyana girman soyayyata ga masoyiyata kuma bangona sannan matata Yetunde ba, wacce jigo ce a rayuwata.

“Ba zan gushe ba wajen ci gaba da kaunar ki da tarairayar ki har abada.

“Ga ’ya’yanmu kuma, Allah Ya amsa addu’arku, domin muna hanyar dawowa gida cike da lafiya.

“Ga sauran ’yan uwa da ma’aikta da abokan aiki na kamfanina, Lakreem Entertainment, da sauran masoya, Allah Ya yi ikonSa, na samu sauki.”

Ya ci gaba da cewa wannan sakon godiyar ya yi shi ne domin godiya ga Allah da kuma matarsa da ta kasance tare da shi a wannan yanayin da ya samu kansa.

Mawakin dai ya ce zai ci gaba da yin irin wannan godiya ga sauran mutane da zarar ya kara samun lafiya.

Bayan bullar labarin rashin lafiyar Eedris din dai, abokin sana’arsa, M.I Abaga, ya nema masa taimakon kudade.