Matar mai zanen tatu ta adana fatar jikin mijinta bayan rasuwarsa

Wani shahararre mai zanen tatu mai suna Chris Wenzel, dan shekara 41 daga kasar Kanada, ya bar wa uwargidansa wasiyya cewa idan ya rasu a adana fatar jikinsa saboda zanen tattu da ya yi, kar a binne shi da shi. Bayan rasuwar Wenzel, matar mai suna Cheryl ta yi kokarin adana fatar jikin mijinta inda […]

Matar mai zanen tatu ta adana fatar jikin mijinta bayan rasuwarsa

Wani shahararre mai zanen tatu mai suna Chris Wenzel, dan shekara 41 daga kasar Kanada, ya bar wa uwargidansa wasiyya cewa idan ya rasu a adana fatar jikinsa saboda zanen tattu da ya yi, kar a binne shi da shi.

Bayan rasuwar Wenzel, matar mai suna Cheryl ta yi kokarin adana fatar jikin mijinta inda ta manna shi a jikin bango.

Wenzel dai ya fara tunanin jinyar da yake yi kamar ba zai warke ba, don haka ya bukaci uwargidansa da cewa, bayan rasuwarsa a adana fatar jikinsa kar a birne shi da ita.

Wenzel yana son ’ya’yansa da jikokinsa su yi sha’awar zanen tattoo da ya yi lokacin da yana raye.

Cheryl, ta bayyana wa kafar yada labarai ta ‘The Globe and Mail’ cewa, da farko wasiyya ta bata mamaki, amma duk da haka ta ce, zata yi bakin kokarinta don cika alkawarin wasiyar da mijinta ya bari.

“Za a iya adana hoto a jikin bango na tsawon lokaci, zanen tatu zane ne da aka yi shekaru daruruwa ana yi kawai za a san yadda za a iya adana fatar, ta yadda zata dade”

A cewar majiyar CTB Saskatoon, an yi binciken lafiyar Wenzel yana dauke da cutar gembon ciki wanda take haddasa masa bugun zuciya. Ya dai rasu ne yana jinya lokacin da yake fama da matsanancin ciwon kirji.

Cheryl ta yi kokarin gano masu sana’ar zanen tattoo daga bisani ta samu yin alaka da masu adana fatar wanda ya rasu da ke da zanen tattoo a Amurka.

Wata da mahaifinta ke da kamfanin zanen tattoo mai suna Kyle Sherwood, ta bayyana wa majiyar CTB Saskatoon cewa, zanen tattoo na bayyana wani tarihi na mutumin da ya rasu.

Kyle ta ce, idan mutum yana da bukatar zanen tattoo abu ne wanda zai kasance tare da shi har karshen rayuwarsa.

Za a iya adana fatar zanen tattoo na Wenzel na kusan wata uku saboda irin hanyoyin da aka bi wajen yin zanen. A cewar Kyle wannan zanen tattoo na Wenzel, ya kasance mafi girman zanen tatu da aka taba adana wa a Arewacin Amurka.

Wenzel nada zanen tatu a fatarsa tun yana da shekara bakwai lokacin da ’yar uwarsa ta gogen nata zanen a fatar jikinta.

Jama’a da dama nata girmama Wenzel ne saboda sha’awar zanen tattoo da ke jikinsa, a duk fadin garin babu wanda zanensa ya shahara kamar na shi.

Matar Wenzel, Cheryl wadda mai gidanta ya zana mata tatu ta ce, ita ma idan ta mutu tana bukatar a adana fatar jikinta kusa da ta maigidanta.

 

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu

Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

CBN ya ƙara kason kuɗin ruwa zuwa 27.25 cikin 100