‘Matar Manomi’
Barkanmu da sake saduwa a wannan fili Manyan Gobe, tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku ‘labarin Matar Manomi’. Labarin na koyawa Manyan Gobe yadda za su zama masu tawakkali a halin da suka sami kansu. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi An yi wani tsohon […]
Barkanmu da sake saduwa a wannan fili Manyan Gobe, tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku ‘labarin Matar Manomi’. Labarin na koyawa Manyan Gobe yadda za su zama masu tawakkali a halin da suka sami kansu. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi
An yi wani tsohon manomi a wani kauye mai kyakyawar mata. Matar tasakkarama ce. Tana sha’awar rayuwar birni da kwadayin zuwa kasuwa ta kashe kudi a kan abubuwa masu kyau. Amma maigidan nata tsoho ne, mai karamin karfi ne, kuma kullum yana cikin jinya. Saboda haka, kullum ranta a bace yake don haka kullum burinta shi ne ta rika saba masa.
Rannan, sai wani ya ji su suna fada har matar ta fita daga gidan tana kuka. Da ganin hakan, sai mutumin ya bi ta. Da ya same ta sai ya ce da ita “ baiwar Allah na ji muryarku da mijinki kuna ta fada ga ki kyakyawa yaya aka yi har kika aure shi gashi yana bata maki rai? Kin ga ni ma aure na ya mutu kuma gashi ina da kudi zan iya biya maki bukatunki in kin yarda za ki bi ni”. Da jin haka, sai ta yarda. Da dare ya yi sai ta kwashe kayanta ta bi wannan mutum.
Washegari da sassafe sai suka kama hanya, a hanyarsu sai suka iso bakin rafi, sai mutumin ya ce da ita “bari in shiga ruwa don na samo mana kwalekwale don ban son ruwa ya taba ki, miko mini kayanki in rike maki don kada barayi su kwace miki kafin na dawo”. Nan take mika masa gwalgwalanta da kudinta ta tsaya a bakin rafi tana jiransa.
Mutumin sai ya ji dadi da ma ba shi da komai anma yanzu ya samu sai ya tafi birni ba da niyyan dawowa ba. Tana ta jiran dawowarsa har rana ta fadi ba ta gan shi ba. Can sai ta hango karen daji bakinsa a cike da nama yana ganin kifaye suna ta tsalle a rafi. Karen daji sai ya ajiye naman bakinsa don ya kama kifi sai ga shaho ya dauke naman da karen ya ajiye. Zuwan shaho sai ya razana kifayen suka nutse cikin ruwa. Nan amarya ta fashe da dariya ta ce “ashe kai wawa ne ga shi ka rasa duka biyun saboda son banza.” Sai Karen daji ya ce da ita “ ai ke kika fi kowa wawanci don kin rasa mijinki, gwalagwalenki da kuma kudinki”.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasin wannan labarin don su kasance masu godiya a duk yadda suka samu kansu.