Matar Rio Ferdinand ta rasu
Matar Rio Ferdinand tsohon kyaftin din Manchester United da kuma Ingila ta rasu. Marigayiyar mai suna Rebecca Ellison ta mutu ne bayan ta yi fama da ciwon daji da aka fi sani da kansa. Ciwon ya harbe ta ne a nono da hakan ya sa ta dauki lokaci mai tsawo tana jinya. ’Yar kimanin shekara […]
Matar Rio Ferdinand tsohon kyaftin din Manchester United da kuma Ingila ta rasu. Marigayiyar mai suna Rebecca Ellison ta mutu ne bayan ta yi fama da ciwon daji da aka fi sani da kansa. Ciwon ya harbe ta ne a nono da hakan ya sa ta dauki lokaci mai tsawo tana jinya.
’Yar kimanin shekara 34, marigayiyar ta auri Ferdinand ne tun a shekarar 2000, inda kawo yanzu suka haifi ’ya’ya uku.
Rio Ferdinand, mai kimanin shekara 36 ne ya bayar da sanarwar mutuwar matar tasa a ranar Juma’ar da ta gabata a shafin sadarwar kulob din kueens Park Rangers na Ingila da yake yi wa kwallo a halin yanzu.
“Ina sanar da ku cewa masosiyata kuma matata Rebecca Ellison ta rasu a yau Juma’a bayan ta yi fama da cutar kansa. Ta rasu ne a asibitin Royal Marsden da ke birnin Landan”.
Marigayiyar ta rasu ta bar mijinta Ferdinand da ’ya’yansu uku masu suna Lorenz mai shekara tara da Tate mai shekara shida da kuma Tia mai shekara hudu.
Tuni ’yan kwallo daga sassan duniya ciki har da dan Najeriya Osaze Odemwingie suka aika masa sakon ta’aziyya na rashin da ya yi.