Matar Sarkin Kano ta rasu
A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne daya daga cikin matan mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ta kwanta dama. Marigayiya Hajiya Rabi, wacce aka fi sani da Umma Uwar Soro ta rasu ne tana da shekaru 67 da haihuwa haka kuma ta rasu ne sakamkon gajeriyar jiyya da ta yi.Ta rasu […]
A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne daya daga cikin matan mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ta kwanta dama. Marigayiya Hajiya Rabi, wacce aka fi sani da Umma Uwar Soro ta rasu ne tana da shekaru 67 da haihuwa haka kuma ta rasu ne sakamkon gajeriyar jiyya da ta yi.
Ta rasu ta bar maigidanta Mai Martaba Sarkin Kano da kuma ’ya’ya biyar. Daga cikinsu akwai Bashir Ado Bayero (dan Lawan) Hakimin Takai da Hajiya Yalwati Ado Bayero matar Matawallen Kano da Tijjani Ado Bayero (Lima) ma’aikaci a rundunar ’yan sandan kasar nan da Umma Ado Bayero da kuma Umar Ado Bayero.
Jama’a da dama ne suka halarci jana’izar marigayiyar wacce aka yi a safiyar Juma’a, wadda kuma babban limamin Kano, Farfesa Sani Zaharadden ya jagoranci gudanar da ita. Daga cikin wadanda suka halarta sun hada da Mataimakin Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi da Sarkin Das, Alhaji Bilyaminu Usman da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano da sauran jama’a.