Matar sarkin Swaziland ta kashe kanta

Daya daga cikin matan sarki Mswati III na kasar Swaziland Senteni Masango mai kimanin shekara 37  ta kashe kanta, inda ake tsammanin ta dauki wannan matakin ne bayan an hana ta zuwa jana’izar kanwarta da ta mutu. An samu gawar Senteni ne a turakarta kwance ba rai a makon da ya gabata. Ita dai Senteni […]

Matar sarkin Swaziland ta kashe kanta

Daya daga cikin matan sarki Mswati III na kasar Swaziland Senteni Masango mai kimanin shekara 37  ta kashe kanta, inda ake tsammanin ta dauki wannan matakin ne bayan an hana ta zuwa jana’izar kanwarta da ta mutu.

An samu gawar Senteni ne a turakarta kwance ba rai a makon da ya gabata.

Ita dai Senteni Masango, kyakkyawar mace ce mai sura mai kyau da ta aura sarki Mswati III na Swaziland a shekarar 2000, inda ta zama daya daga cikin matansa guda 15 da sarkin ke zama da su, sannan kuma rahotanni daga kasar sun nuna cewa dama tana zaune ne cikin takura da damuwa na tsawon lokaci.

Ita dai sarauniya LaMasango, kamar yadda ake kiranta bayan ta auri sarkin, ta auri sarkin ne a shekarar 2000 tana ‘yar shekara 18  bayan an zabo ta daga cikin ‘yan mata da aka kawo ya sarki ya zaba a wani bikin raye-raye da ake shirya wa ’yan mata da suka tasa, sannan kuma suna da ‘ya’ya biyu tare.

An gudanar da bikin sarauniya LaMasango ne a wani kwaryakwaryar biki saboda ba a so a bayyana bikin a lokacin, sannan kuma rahotanni na nuna cewa tun bayan auren, ba ta samu kwanciyar hankalin zama a gidan ba a matsayin matar sarkin wanda shi ne sarki na karshe mai irin mulkinsa a yankin Afirka baki daya.

Wannan ya sa take ja baya a duk harkokin masarautar, ko zaman fada ake yi, ita sai ta kuma gefe kamar yadda makusancin masarautar ya sanar. Sannan ta fara neman duk abin da zai rika debe mata kewa irinsu zane-zane da kwalliyar fuska da jiki da dai sauransu domin ta rika samun saukin rayuwa a gidan.

Da yake magana a game da mutuwarta, wani makusancin sarkin, Chief Lusendbo Fakudze, ya ce sarkin na matukar mamakin mutuwar matarsa, “mun samun labarin cewa wai kashe kanta ta yi, amma ina tunanin wannan maganar ba gaskiya ba ce,” inji Fakudze.

“Har yanzu sarkin na jimami tare da mamakin mutuwar sarauniya LaMasango domin sun kasance cikin jin dadi da soyayyar juna.

A cewar Chief Fakudze, sarkin ya kasa halartar bikin binne marigayyar na dare domin har aka binneta yana gida yana zaune

An dade ana kushe sarkin mai kimnin shekara 50 a duniya, bisa yadda yake rayuwar albazaranci da dukiya duk kuwa da cewa mutanensa suna cikin wahala da talauci.

Ana rade-radin cewa yana da ’ya’ya 23, kuma fadarsa na kusa da babban birnin kasar Swaziland ne wato Lobamba.

Sarki Mswati ya yi karatu a Ingila a makarantar Independent Sherborne kafin aka zabe shi ya zama sarki a shekarar 1986 yana dan shekara 18 a rayuwa jim kadan bayan ya kammala karatun Sakandari a Ingila.

A shekarar 2002, Hukumar Amnesty International ta zargi sarkin da masu goya masa baya wajen tauye hakkin dan Adam, bayan sun dauki wata yariya ’yar shekara 18 a rayuwa mai suna Zena Mahlangu da karfin dole daga makarantar da take karatu sannan suka tilasta mata auren sarkin.

A lokacin mahaifiyar Zeena ta yi kokarin kai sarki Mswati kotu domin a kwato mata hakkinta a dawo mata da ’yarta, amma abin ya ci tura. Hakanan don dole ta ci gaba da zama da sarkin.

Auren da ya yi na karshe shi ne aurensa da Siphelele Mashwama, yar shekara 19 a rayuwa, kuma diya ce ga daya daga cikin ministocinsa, wadda ya aura a watan Satumbar bara.

Matansa guda biyu sun samu nasarar barin gidan, Putsoana Hwala da Delisa Magwaza.

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu