Matar Shugaban kasa ki sani Arewa ita ce gatan Najeriya

Turawan mulkin mallaka sun tarar da yankin Arewa bisa kyakkyawan tsarin shugabanci, tattalin arziki da zamantakewa mai kunshe da girmama juna. karkashin jagoranci sarukunan gargajiya da malaman addini. Wannan ya ba wa Turawan mulkin mallaka damar sarrafa al’ummar yankin cikin ruwan sanyi, ba tare da fuskantar wani kalubale ba ta hanyar amfani da sarakunan gargajiya, […]

Matar Shugaban kasa ki sani Arewa ita ce gatan Najeriya
Matar Shugaban kasa ki sani Arewa ita ce gatan Najeriya

Turawan mulkin mallaka sun tarar da yankin Arewa bisa kyakkyawan tsarin shugabanci, tattalin arziki da zamantakewa mai kunshe da girmama juna. karkashin jagoranci sarukunan gargajiya da malaman addini. Wannan ya ba wa Turawan mulkin mallaka damar sarrafa al’ummar yankin cikin ruwan sanyi, ba tare da fuskantar wani kalubale ba ta hanyar amfani da sarakunan gargajiya, sabanin yankin Kudu da kowa yake zaman kansa. Yankin Arewa ya bayar da gagarumar gudumowa wurin ’yanto kasar nan daga kangin bauta ta Turawan mulkin mallaka.

Duniya ta shaida kyakkyawan misalin shugabanci mai cike da adalci da shugabannin kasar nan na farko ’yan Arewa suka shinfida a zamanin mulkinsu. Sun yi mulki ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Har zuwa yau, kasar nan ta kasa samun madadinsu. Bayan gano man fetur, yankin Arewa ya dauki nauyin hako shi ta hanyar bayar da kudin albarkatun noman gyada da auduga da ridi da kuma kirgin dabbobi. Bayan barkewar yakin Basasa (1967-70) sojoji ’yan Arewa sun taka muhimmiyar rawa don ganin kasar nan ba ta wargaje ba, ta fuskar
sadaukar da rayuwarsu gaba daya don murkushe ’yan tawayen Biyafara. Musamman kwamandojin runduna ta daya da ta biyu Janar Murtala Muhammad da Janar Mamman Shuwa.
Na yi wannan takaitacciyar shinfida ne domin a fahimci matsayin da Arewa ta taka wurin gina wannan kasa tamu Najeriya. Matar Shugaban kasar Najeriya ta yi furici mai cike da nuna kabilanci ga al’ummar Arewa da sunan siyasa. Ita dai Dame Patience Jonathan ta ce, “Mu a Kudu ba mu da almajirai, matanmu ba sa haihuwar ’ya’ya barkatai, mu matanmu ba sa haihuwar ’ya’ya su watsar da su a kan titi. Don haka ba ma son mutane daga wancan sashe”. Wadannan kalamai da suka fito daga bakinta, abin Allah wadai ne, abin takaici!. Wannan cin mutunci ne da keta alfarmar mutuntaka da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar wa kowane dan kasa ba tare da nuna wani bambanci ba. Ya kamata kowane dan Arewa ya yi Allah wadai da wannan kalaman nata a kanmu. A matsayinta na matar shugaban kasa bai kamata kalamai irin wannan su rika fita daga bakinta ba, na nuna kabilanci ga wani sashe na al’ummar da suke mulka.
Mu mun gode Allah da ya halicce mu a wannan yanki na Arewa, ki sani yankinmu mai albarka ne da Allah ya albarkace shi da dukkan wani nau’in albarkatun kasa. kasarmu mai albarka ce da fuskar noma, da kowace jiha daya za ta iya ciyar da kasar nan. Ki sani ’ya’yan da kike yi wa kallon ana haihuwa barkatai ko a na jefarwa a kan titi, masu albarka ne. Akwai da dama da Allah ya daukaka su a duniya ta fannoni da dama na rayuwa. A yau daya daga cikin attajiran duniya, bakin fatar da ya dade yana rike da kambu na daya da ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika watau Aliko dangote dan garin Kano ne na Arewacin kasar nan. Bakin fatar da ya yi fice a duniya wurin zayyana mota a duniya Jelani Aliyu dan Sakkwato ne .
Sannan shugaban kungiyar ba da shawara a kan harkokin ruwan sha na Najeriya da kuma na Afrika, sannan a lokaci guda shugaban kungiyar albarkatun ruwa ta Afrika da ke da hedikwata a Nairobin Kenya, Injiniya Mustapha Bukar dan garin Daura ne ta jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin kasar nan. Kai akwai mutane masu yawan gaske da ke shugabantar kungiyoyi da ma’aikatu daban-daban a ciki da wajen kasar nan, wanda lokaci ba zai ba da damar lissafo su ba. Mutane masu yawa sun ciyo kyaututtuka na duniya a fannoni da daman a rayuwa. Muna nusar da ke giyar mulkin da ta kwashe ki har kika yi wannan katobarar, ai dan Arewa ne ya share wa mijin naki hanyar darewa bisa mulkin.
Ba wannan ba ne karo na farko da ku ke shiriftu da katsalandan, a cikin tsarin mulkin kasar nan ke da ’yan barandar mijinki irin su Asari Dokubo. Ba za mu manta ba da irin kalamin da kika yi a lokacin sace ’yan matan Chibok ba, na rashin nuna tausayi a gare su a matsayinki. Jama’a kuke nema fa a zaben da ya taho, sannan mu Arewa muna da jihohi goma sha tara (19) banda Abuja daga cikin jihohi talatin da shida (36) na kasar nan. Shugabanni goma sha biyar da suka mulki kasar nan guda takwas ai ’yan Arewa ne.Saboda haka kuri’armu tana da matukar muhimmanci wurin cin zaben shugaban kasar nan. Amma lokaci zai nuna idan muna da tasiri ko babu.
Injiniya Jibril Abdul Daura
08038997861,08022997340