Matar shugaban Nicaragua za ta zama mataimakiyarsa
Shugaban kasar Nicaragua Daniel Ortega ya zabi matarsa domin zama mataimakiyarsa a zaben shugaban kasar da ya tsaya a karo na uku.Dama dai matar tasa, Rosario Murillo, tana da babban mukami a kasar domin kuwa ita ce mai magana da yawun shugaban kasar, kuma ana yi mata kallo a matsayin wadda ke taya shugaban gudanar […]
Shugaban kasar Nicaragua Daniel Ortega ya zabi matarsa domin zama mataimakiyarsa a zaben shugaban kasar da ya tsaya a karo na uku.
Dama dai matar tasa, Rosario Murillo, tana da babban mukami a kasar domin kuwa ita ce mai magana da yawun shugaban kasar, kuma ana yi mata kallo a matsayin wadda ke taya shugaban gudanar da mulki, kamar yadda BBC ta bayyana.
Kusan kullum sai ta bayyana a gidan talabijin din kasar domin bayar da bayani kan wasu shirye-shiryenta.
Shi kuwa Shugaba Ortega ba kasafai yake fitowa bainar jama’a ba.
Wasu dai na sukar matar da mijinta kan wannan batu, suna masu cewa sun mayar da mulkin kasar kamar gadon gidansu.
Rosario Murillo, wacce ta haifa wa shugaban kasar ‘ya’ya bakwai, ta kware wajen magana da harshen Turanci da Faransanci, baya ga matsayinta na fitacciyar marubuciyar waka.
Har ila yau, ta yi fice wajen sanya tufafin kawa da gwala-gwalai wadanda aka saba gani a shekarun 1960.
A watan Nuwamba ne dai aka gudanar da zabe a kasar wanda take yankin Latin Amurka.