Ambaliyar Maiduguri: Matar Tinubu ta ba da kyautar N500m

Oluremi Tinubu ta ce ambaliyar “al’amari ne daga Allah,” ta ƙara da cewa “Allah ne Kaɗai Zai iya mayar musu da asarar da suka yi.”

Ambaliyar Maiduguri: Matar Tinubu ta ba da kyautar N500m

Sanata Oluremi, matar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 500 domin tallafa wa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Oluremi Tinubu, wacce uwargidan mataimakin shugaban kasa, Nana Kashim Shettima ta wakilta, ta sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da ta kai ziyarar jaje ga gwamna Babagana Zulum a gidan gwamnati Borno da ke Maiduguri.

Da take bayyana damuwarta game da ambaliyar, ta bayyana hakan a matsayin “al’amarin Allah,” ta kara da cewa “Allah ne Kaɗai Zai iya mayar musu da asarar da suka yi.”

Ta kuma kai ziyarar jajantawa Fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai Al-Amin El-Kanemi, wadda ita ma ambaliyar ruwa ta mamaye.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta