Matar wani likita ta kamu da Ebola a Fatakwal
Matar wani likita da Ebola ta kashe a Fatakwal ta Jihar Ribas ta kamu da kwayar cutar.Kwamishinan Lafiya na Jihar Mista Sampson Parker, ya ce, bincike ya nuna matar wadda mijinta Dokta Ike Enemo ya rasu a ranar 22 ga watan Agustan da ya gabata sakamakon kamuwa da Ebola, ita ma ta harbu da cutar.Mijin […]
Matar wani likita da Ebola ta kashe a Fatakwal ta Jihar Ribas ta kamu da kwayar cutar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Mista Sampson Parker, ya ce, bincike ya nuna matar wadda mijinta Dokta Ike Enemo ya rasu a ranar 22 ga watan Agustan da ya gabata sakamakon kamuwa da Ebola, ita ma ta harbu da cutar.
Mijin nata ya kamu da cutar ce bayan da ya yi jiyyar wani ma’aikacin kungiyar kasashenAfirka ta Yamma (ECOWAS), da ya yi mu’amala da Mista Patrick Sawyer dan kasar Liberiya da ya kawo cutar Najeriya.
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Legas, ta ce an dawo da matar Legas, ana kula da ita a wata cibiya ta masu fama da cutar.
Hukumomi sun binciki sama da mutum 200 da suka yi mu’amala da matar.
Wannan shi ne karon farko da cutar ta Ebola ta yadu a wajen Jihar Legas.