Matasa 150 Sun Halarci Gasar Kirkire-Kirkiren Fasaha a Kano
Aƙalla matasa 150 masu kirkire-kirkire daga yankin Arewa sun hallara a Kano don halartar “Innovate North” Business Development and Innovation Hackathon, wani shiri da ke da nufin ƙarfafa harkokin kasuwanci da sauya fasalin dijital. Yayin da take jawabi a taron, Maryam Lawan Gwadabe, wacce ta shirya gasar kuma ita ce wanda ta kafa Blue Sapphire […]
Aƙalla matasa 150 masu kirkire-kirkire daga yankin Arewa sun hallara a Kano don halartar “Innovate North” Business Development and Innovation Hackathon, wani shiri da ke da nufin ƙarfafa harkokin kasuwanci da sauya fasalin dijital.
Yayin da take jawabi a taron, Maryam Lawan Gwadabe, wacce ta shirya gasar kuma ita ce wanda ta kafa Blue Sapphire Hub, ta jaddada mahimmancin shiryawa da ba da jagora ga matasa domin bunkasa basirarsu.
- APC ta kori tsohon Gwamnan Osun, Aregbesola daga jam’iyyar
- Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara
“Yawancin matasa masu kirkire-kirkire ba su da jagora ko kuma wanda zai taimaka musu su sauya tunaninsu zuwa kasuwanci mai ɗorewa,” in ji ta.
Gwadabe ta bayyana gasar a matsayin babbar dama da ke bai wa matasa ‘yan Najeriya zarafin nuna fasaharsu a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire.
Gasar ta ƙunshi kungiyoyi 30 — kowacce tana da mutum biyar, inda suka nuna basirarsu a bangaren dijital da kasuwanci a cikin yanayi na gasa.
Da yake wakiltar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Yusuf Kofar Mata, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na da cikakken shirin tallafa wa matasa a fannin kirkire-kirkire da fasahohin zamani.
Ya bayyana cewa gwamnati na da shirin horar da mutum miliyan ɗaya a fannin fasahar sadarwa ta ICT kafin ƙarshen wa’adin mulkinsu.
“Abin alfahari ne ganin matasa maza da mata suna bada gudunmawa a fannin kirkire-kirkire na zamani.
“Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da tallafa musu, kuma Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na da shirin ciyar da wannan fanni gaba cikin shekara guda,” in ji Kofar Mata.
Ya kuma jaddada cewa fasahohin zamani na da gagarumin tasiri a tattalin arziki, inda ya buƙaci matasa su yi amfani da fasaha ta hanyoyin da za su amfane su, tare da cin moriyar damar da ke cikin ɓangaren ICT.
“Kafin ƙarshen wannan wa’adin mulki, muna da shirin horar da mutum miliyan ɗaya da fasahar dijital, domin su sami abin dogaro da kansu tare da bada gudunmawa wajen ci gaban Kano da Najeriya gaba ɗaya,” in ji shi.