Matasa 17 sun shiga hannun hukuma kan fashi da sara-suka

Rundunar tsaro ta Operation Safe Haben (OPSH) da ke Jos ta kama matasa 17 bisa zargin kisan kai da fashi da makami da sara-suka da tayar da zaune-tsaye da yin damfarar kudi da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.  A lokacin da rundunar ke nuna matasan da ake zargi da aikata wadannan laifuffuka a hedikwatarta […]

Matasa 17 sun shiga hannun hukuma kan fashi da sara-suka

Rundunar tsaro ta Operation Safe Haben (OPSH) da ke Jos ta kama matasa 17 bisa zargin kisan kai da fashi da makami da sara-suka da tayar da zaune-tsaye da yin damfarar kudi da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba. 

A lokacin da rundunar ke nuna matasan da ake zargi da aikata wadannan laifuffuka a hedikwatarta da ke Jos, Kakakinta Kyaftin Umar Ahmad Umar ya ce an kama wadanda ake zargi da fashi da makami ne a Hawan Kibo da ke hanyar Jos zuwa Abuja, yayin da aka kama wadanda ake zargi da laifin sara-suka da kisan kai da mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da sauran laifuffuka a garin Jos da karamar Hukumar Mangu da kauyen Miyango da ke karamar Hukumar Bassa da sauran garuruwan Jihar Filato.

“Mun kama matasan da ake zargi da aikata wadannan laifuffukan ne daga watan Agusta zuwa Satumba, inda bayan mun nuna su za mu mika su ga hukumomin da suka fi dacewa don su gudanar da bincike, tare da gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.

Kyaftin Umar ya ce a cikin matasa 17 da suka kama, biyu daga cikinsu ana zarginsu ne da neman tayar da zaune-tsaye a kauyen Miyango da ke karamar Hukumar Bassa, inda aka samu yamutsi a kwanakin baya.