Matasa 172 sun haukace saboda shan kwaya a Zamfara
Shan miyagun kwayoyi ya haukata matasa 172 a Jihar Zamfara cikin shekara shida da suka gabata. Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ce ta sanar da haka a jihar ta bakin mataimakin kwamandanta na sashen yaki da miyagun kwayoyi na jihar, Ladan Hashim. Wani saurayi dan acaba ya mayar da N20m […]
Shan miyagun kwayoyi ya haukata matasa 172 a Jihar Zamfara cikin shekara shida da suka gabata.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ce ta sanar da haka a jihar ta bakin mataimakin kwamandanta na sashen yaki da miyagun kwayoyi na jihar, Ladan Hashim.
- Wani saurayi dan acaba ya mayar da N20m da ya tsinta
- Gwamnati ta yi gwanjon rigar nonon Diezani a kan $12.3m
Ladan ya ce, “Matasa da dama na tsare a gidajen yari, wasu a gidajen kula da lafiya, yawancinsu kuma na fama da cututtukan kansar makogwaro, cutar hanta da cutar koda da sauransu.
“Mafita ita ce a tabbatar da cewa kowa yana amfani da magunguna yadda ya dace kamar yadda kwararrun likitoci suka tsara mana,” inji shi.
Ya ce a cikin wata taran da suka gabata hukumar ta tsare mutum 221 kan shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar, ta kuma yi wa wasu 152 jan kunne.
“Saboda haka akwai bukatar hadin kai, fahimta da taimako domin bayar da dauki a kan kari da yi msusu magani da kuma dawo da su cikin al’umma.
“Dukkansu suna bukatar samun daukin da ya dace a wurin da ya dace kuma a kan lokaci.”