Matasa 5 sun rasu a hatsarin mota a Birnin Kebbi
Gwamnatin jihar ta ya bayar da cekin tallafin Naira miliyan 20 ga iyalan mamatan, miliyan daya ga duk wanda ya samu rauni da kuma miliyan biyu ga sauran ’yan cikin motar.
Matasa biyar daga yankin Ambursa sun rasa rayukansu a bayan motar da suke ciki ta yi adungure a kan titin Filin Jirgin Sama da ke Karamar Hukumar Birnin Kebbi ta jihar Kebbi.
Wanna mummunan haɗarin mota ya faru ne lokacin da motar da ke ɗauke da matasa 18 take kai hanyar kai su wasan sada zumunta ta kwallon kafa.
Hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar matasa biyar, yayin da sauran suka samu raunuka daban-daban.
A yayin ziyarar ta’aziyya a fadar Hakimin Ambursa a madadin Gwamna Nasir Idris, Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Abubakar Umar Dutsinmari, ya ce a kan idon gwamnan abin ya faru, inda ya shiga kai tsaye aka yi aikin ceto tare da shi.
- An kama dan sanda kan yi wa ’yar shekara 13 fyade
- Matar aure ta yi yinƙurin yi wa mijinta yankan rago a Kastina
- Daliban FUT Minna sun kulle VC a waje kan matsalar fashi da makami
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin gaggawa domin tabbatar da cewa an ba wa waɗanda suka jikkata kulawar da ta dace.
Dutsinmari wanda ya kai kai ta’aziyyar tare da kwamishinan yada labarai da ayyuka ya bayar da cekin tallafin Naira miliyan 20 ga iyalan mamatan, miliyan daya ga duk wanda ya samu rauni da kuma miliyan biyu ga sauran ’yan cikin motar.
Hakimin Ambursa, Alhaji Isah Haruna Rasheed, ya bayyana matukar godiya ga Gwamna Nasir Idris bisa saurin daukar mataki da kuma taimakon kuɗi da ya bayar ga waɗanda hatsarin mota ya rutsa da su.