Matasa a guji rikicin siyasa

Dole ne in ma kaina adalci, don ba zan ci zamani na. inci na wani ba, don haka ba zan kira kai na matashi ba. Hausawa na cewa in an girma, a san an girma, don Allah a rinka tunani, kuma ni dai ba aiki za a daukan ba, ballantana in rage shekarun haihuwata; ba […]

Matasa a guji rikicin siyasa
Matasa a guji rikicin siyasa

Dole ne in ma kaina adalci, don ba zan ci zamani na. inci na wani ba, don haka ba zan kira kai na matashi ba. Hausawa na cewa in an girma, a san an girma, don Allah a rinka tunani, kuma ni dai ba aiki za a daukan ba, ballantana in rage shekarun haihuwata; ba kuma takara zanyi ba. Allah suturi bukwai in ji kishiyar mai gwaiwa.

A tawa shawarar duk wanda ya dara shekara 35 ya fitar da kansa daga sahun matasa. A ganina in ya dara shakaru 40 kuma yana kiran kansa matashi, bai gode wa Allah ba. Don shekaru rahama ne. idan ka same ka zama mai godiya ga Rabis samawati.
Don a cikin wadannan shekarun komai dakikancinsa dole ya ilmantu da darasin yau da gobe, kuma dole akwai ilmin da ya samu na rayuwar duniya, wanda za a iya amfanuwa da shi. To na me Allah ya yi mini baiwa da shekaru zan zama butulu? Dalilai marasa tushe kansa ’yan sama da shekara 40 kiran kansu matasa. Ni ba matashi ba ne. don na daranma shekaru 40, na yi aure, ina da shekaru 25. Ina da shekaru 24, na samu dana na farko.wanda ya rasu bayan watanni da haihuwarsa.
Ina da 25 na haifi dana na biyu. kuma yana raye, yana karatu, yana yawan cika man gida da matasa. Sai in dawo cikin abokansa, in ce ni matashi ne? Kasan rayuwarmu ba ta ’yan bariki ba ce. Don haka tun kafin in haifi dana na farko marigayi. Da na biyu. Dan matashi.ina rike da yara biyu mata. Ina da shekaru 23, dayansu na da shekaru biyu, daya watanni tara. Wadannan yaran duk an aurar da su, suna auren wasu matasan. Shi ke nan sai in dawo cikin surukaina, in ce ni ma matashi ne? Babu godiya a ganina, duk wanda ya haura 40 ya kira kansa matashi. Domin ko a cikin Musulunci shekaru 40 na daga cikin shekarun cikar hankali; ko Bature cewa ya yi wawan shekara 40, wawa ne har abada.
Daga shekaru 40 zuwa 55 kamata ya yi mutum ya zama tsaka-tsakin mai bai wa matasa shawara. Daga shekaru 55 zuwa 70 dattijo daga 70 zuwa sama tsoho. Allah yasa mu zama dattawan kirki, mu kuma yi tsufa mai kyau. Don kuwa duk matashin da bai yi rayuwar kirki ba. zai zama dattijan banza; zai kuma tsufa a wulakance, zai mutu cikin kaskanci. Allah Ya kiyaye mu.
A matsayina na mai bai wa matashi shawara, kanyadda zaben nan ya taho, zan shaida masa cewa, ‘duk wani dan sama da 40 idan ya shigo cikin wadanda ya kamata ya ba mu shawarar kirki bai ba mu ba, zan dauke shi a mutumin banza? In dattijo ne na banza, in kuma tsoho ne, wanda tsufa ya yi gardama, to ya zama tsohon banza.
Ba zan yarda da wanda zai ce inje gidan wani da muke da bambancin ra ‘ayi in kai farmaki ba. Domin sau da yawa irin wadannan hare-haren ana kai su ne domin hassada kawai, sai a ce bari rikici ya barke na siyasa, gidan wane da wane sai mun kona su. Matasa su sani mafi yawa daga cikin hankoron taba dukiyar wani hassada ce kan kawo ta, kuma ba wani amfani wannan zai yi a nuna fushin zabe. Wane wannan zai iya canzawa? Da ina cikin matasa ba zan bari a yi amfani da ni a kone-kone domin zabe ba.
Da ina cikin Matasa ba zan bari ai amfani dani wajen kona kayan gwamnati ba. Don kuwa kayan gwamanti ai kayanmu ne. kuma kaso na kudin kasa, wanda ina da kaso a ciki.don haka bazan kona, ba. ba zan bari a kona ba.
Dole matashi ya sani mulki canzawa yake , amma kayan gwamnati suna nan. Idan mai mulki ya tafi dole ya bar aikin da ya yi. Ya yi kadan kai a gidansu. Ko dakinsa. Don haka amfaninsa yana ga wadanda aka yi mawa.
Tunda kayan gwamnati kayanmu ne name zan taba su ko in bari a taba su? Matashi ya sani idan aka yi rikici, shi mai mulki ya saci kudinmu. Zai tada hannunsa ne, ya kara gaba. Mu zai bari , wadanda aka yi wa sata. Sai kuma abin da Allah ya kwatar mana daga aikin da aka yi na kudinmu da aka ba su.
Don haka zan kare aikin don nasan shi ne kawai abin da zan tsira da shi. Farmaki kan kayan gwamnati ba dubara ba ce, amma ci gaba ne, na mai hakar rijiya. Don haka ni ba da ni ba, ba taba kayan gwamnati, don kuwa kai na zan yi mawa, idan ni matashi ne.
Da ina cikin matasa ba zan kai wa wadanda ba addininmu daya, ko wadanda muke da bambancin kabila farmaki ba. Wai ma saboda me? Saboda siyasa? Ai wani rai ba ya daukar laifin wani rai.’ Kuma idan na kai hari ga wasu aka kai wa ’yan uwana a wani wuri; me aka yi ke nan? Idan da ni matashi ne, duk wanda ya yi safarar kwaya in sha, in yi bangar siyasa, don hankali na ya fita in aikata abin da yake nema, ba zan sha ba. amma kuma zan yi kamar na sha in koya masa hankali, in ce ai ina cikin maye ne.
Da ina daga cikin Matasa zan yi amfani da hankalina , ga duk abin da zanyi, zan tsara nuna fushina a tsanake, yadda zai yi tasiri, kuma ya yi amfani, ba tare da cewa na gwada ni ba ni da wayewa ba.
Wannan ’yar shawarar na yi ta ga ’yan kannenmu na Katsina, amma in matashi wata shiyya ya karanta ya ga abin amfani masha Allah, kowa na iya amfani da ita. Gaskiyar magana, wannan shawara tawa mai tsada ce, don har na so in ce banda Bagobiri da Banufe da Bahadeje. Duk da cewa wadannnan bayinmu ne, na amince matasansu su yi amfani da ita. Danjuma Katsina, dan jarida ne marubuci dake zaune a Katsina.08035904408 email [email protected]

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi